LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

'Na dade ina shawa'arta da jiran dama'; a cewar wanda ya fyade gyatuma 'yar 80


Wata gyatuma mai shekaru 80 a yankin Phatthalung a kasar Thailand tana gida a kwance ana yi mata karin ruwa bayan wani mutum mai shekaru 50 da ya yi mata fyade a ranar 21 ga watan Yuli.

Wacce abin ya faru da ita ta shaidawa manema labarai cewa tana sayar da shinkafa ne a cikin ganyen ayaba sai wani mutum mai kimanin shekaru 50 ya iso inda ta ke. Ta ce ya rika yi mata hira mai sanyaya zuciya inda ya ce ya dade yana kaunar ta tun lokacin tana da kuruciyya a yayin da suke makwabtaka.

Ya fada mata cewa zai siya dukkan shinkafar amma za ta bi shi zuwa gidan dan uwansa inda zai basu abincin. Sun yi ciniki sun amince zai biya ta Bt2,000 (S$90). A hanyar su na zuwa gidan yan uwan nasa sai ya canja hanya ya tsawa a wani kango,

a cewar ta. Nan take ne ta fahimci abinda ya ke niyyar aikatawa kuma ta yi kokarin tserewa amma ta kasa. Ta ce bayan ya gama yi mata fyade ya kuma sace karamin jakar ajiyar kudaden ta. Yan uwan, a halin yanzu suna neman yan sanda su binciko mutumin su kama shi da gaggawa.

Yan sandan a ranar Talata sun ce sun fara tattara bidiyon da naurorin tsaro na CCTV suka dauka kuma sun fara yi wa mutanen unguwar tambayoyi da niyyar samun bayani da zai tamaka a kama mutumin. A wani labarin, wata kotu da ke zamanta a jihar Ebonyi ta umurci a bawa wani Nwali Kingsley,

masauki a gidan kaso a ranar Talata saboda kashe wani Nwafor Johnson yayin masa gwajin shiga kungiyar asiri. An gano cewa wanda ake zargin da wasu da ake nema har yanzu sun kuma azabtar da wani Chigbo Ugbala da sanduna da adduna yayin gwajin ta shiga kungiyar asirin. Punch Metro ta ruwaito cewa bayan Johnson ya mutu an jefa gawarsa a cikin rafi,

Ugbala ya tsere daga wurin da ake gwajin shiga kungiyar asirin. Wata majiya ta ce anyi kokarin gano gawar mamacin daga rafin amma ba ayi nasara ba.

Wakilin majiyar Legit.ng ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 10 ga watan Yuli a makatantar sakandare ta Ekeugwu-Azuinyaba da ke karamar hukumar Ishielu na jihar Ebonyi. An gurfanar da Kingsley a kotun ana tuhumarsa da kisan kai, hadin baki, shiga kungiyar asiri da mallakar bindigu ba tare da izinin hukuma ba.

SOURCE: LEGIT.NG

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments