--
Duba Yadda ake hada-hadar ragunan layya a Najeriya

Duba Yadda ake hada-hadar ragunan layya a Najeriya



Yayin da Babbar Sallah ta matso sosai, hada-hadar raguna da sauran dabbobin layya ta kankama a sassan Najeriya.

Aminiya ta zagaya sassan kasar domin gano farashin raguna da yanayin hada-hadar dabbobin a kasuwanni daban-daban.

A akasarin jihohin da Aminiya ta ziyarta, masu sayar da raguna sun ce dabbobin sun yi tsada, in banda a wasu jihohin ‘yan kalilan.

Yawanci sun ta’allaka karancin sayen dabbobin da rashin kudi a hannun mutane wanda kullen COVID-19 ya haifar.

Kano babu ciniki sosai
A babbar kasuwar dabbobi ta ‘Yan-Awaki da ke Kano, Aminiya ta iske dabbobi jibge, ga kuma masu saye suna ta hada-hada.

Dubun dubatar raguna a kasuwar dabbobi a Kano
Wani mai sayar da dabbobi a can, Malam Ali Ahmed, ya ce duk da karancin cinikin a bana sukan sayar da dabbobi kusan 1,000 a kullum.

“Mukan loda kimanin tirela bakwai zuwa takwas ta dabbobi a kullum a ‘yan kwanakin nan domin kaiwa wasu jihohin musamman na Kudancin Najeriya”, inji shi.

Game da farashin raguna a kasuwar, ya ce manyan kan kai N180,000 zuwa N200,000, matsakaita kuma N65,000 zuwa N75,000 sai kanana da ke kai kimanin N15,000.

Ya kara da cewa yawanci sukan sayo dabbobin ne daga jihohin Arewa maso Gabas da ma wani bangare na Jamhuriyar Nijar.

Mutane ba su da kudi
Wani mai sarin raguna yana kaiwa Kudancin Najeriya, Mohammed Sani Kofar Wambai ya ce ragon da suka saya dubu 40 a bara, bana baya wuce dubu 35.

“Ana ciniki sosai Alhamdulillah amma bara gaskiya an fi ciniki saboda rashin kudi a hannun mutane”.

A kasuwar dabbobi da ke Hotoro Tunshama kuwa, Malam Abdullahi Muhammad Kawon Kudu mai sayar da raguna ya ce sukan taba ciniki duk da karancin kudin da mutane ke yi a bana.

Kasuwar dabbobi ta ‘Yan Awaki a Kano
Shi kuwa wani mai sayen rago a kasuwar ta Tunshama, Malam Halilu Ahmad ya ce bara raguna biyu ya yanka, amma bana guda daya zai yi layyar.

“Akwai makwabtana da suke yankawa duk shekara amma bana sun yanke shawarar kawai su hada kudi su sayi sa su yanka su yi watanda saboda ba za su iya sayen ragunan ba duk kuwa da cewa sun fi sauki a bana.

Raguna sun yi tsada a Kaduna
A Kaduna kuwa, wasu masu sana’r dabbobi shaida wa Aminiya cewa an samu karin farashin dabbobi a bana saboda rufe kan iyakokin kasa da kuma karuwar darajar Dala a kan Sefa.

A cewarsu, yawancin dabbobin ana shigo da su ne daga kasashe makwabta masu amfani da kudin Sefa.

Amma shugaban masu sayar da dabbobi a Kasuwar Zango, Malam Hassan Saleh ya ce a dabbobin ba su yi tsada kamar yadda ake fadi ba, duk kuwa da yanayin da ake ciki.

Wata kasuwar dabbobi a Kaduna
A cewarsa, a kasuwar farashin manyan dabbobi ya fara ne daga N40,000 zuwa 100,000.

“Gaskiya farashin dabbobi ya dan tashi saboda tsadar Dallar Amurka. Domin masu safarar su zuwa cikin kasa sai sun canza kudin zuwa kudin Sefa wanda hakan ke sa farashin tsada.

Aminiya ta fahinci cewa duk da tashin farashin dabbobin akwai kuma yan madaidaita da suka fara daga N18,000 zuwa N35,000.

Malam Muhammadu Siasia ya ce, “Ni na shiga kasuwar ta Zango kuma na samu yan dubu 20,000 masu kyau na saya. Saboda haka karfin aljihun mutum daidai ragon da zai saya”.

‘Masu sayar da raguna na jira a yi albashi’
Manyan dillalan raguna da sauran dabbobi a shahararriyar kasuwar dabbobi ta Kasuwar Shanu a Maiduguri da sauran kananan kasuwanni na kukan rashin masu aikin albashi a kasuwannin.

Modu Kukawa wanda ke sayar da dabbobin a kasuwar wucin-gadi da ke kan Titin Baga ya danganta hakan da rashin biyan albashin ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu.

“Ga raguna nan daban-daban amma babu masu saye. Mutum zai zo kasuwar nan tun ranar Juma’a amma bai wuce ya sayar da raguna uku ko biyar ba a kullum.

“Mun kawo kusan tirela daya ta raguna wannan kasuwar da sauran kasuwanni amma aka shaida mana cewa ba za mu yi ciniki ba saboda gwamnati ba ta yi albashi ba”, inji Modu.

Kudin babban rago a Maiduguri yana kamawa daga N150,000 zuwa N170,000. Matsakaici kuma daga N70000 zuwa N80,000, karami kuma ba ya haura N40,000.

Sai dai Modu ya yi hasashen cewa farashin na iya tashi da zarar aka biya albashi a jihar.

‘Bana dabbobi sun fi tsada a Sokoto‘
Shugaban kungiyar masu sayar da raguna da awaki na Sokoto Alhaji Isa Bello Unno Sabon Birni ya shaida wa Aminiya cewa bana yanayin kasuwar dabbobi sai godiyar Allah.

“Ba mu fatan farashi ya fi yanda yake a yanzu ba duk da alamu sun nuna babu hakan don an  dauki raguna 1,000 cikin kasuwar nan tamu ta Kara zuwa kasar Nijar

“Kamar yadda muka saba duk sati muna kai musu, dabbobinmu sun fi nasu mai; ga shi kuma kudinsu waton Sefa ta dara farashin Naira.

“A wannan shekarar ma abincin dabbobi ya yi tsada, kan haka farashin dabbobi bai wani haurawa ba, kana iya samun ragon da za ka yi layya da shi a matakin farko N35,000 zuwa N45,000.

“Matsakaici za ka iya samu N60,000 zuwa N100,000, manyan raguna na alfarma kuma N250,000 zuwa N300,000; a haka za ka samu”, a cewarsa.

‘A rangwanta wa masu sayen raguna’
Alhaji Isa ya ce shekara uku da suka gabata kasuwancin ya suya daga yadda a shekarun baya suke fara hada-hadarsu tun sallah saura kwana 30, amma yanzu sati daya ne suke ciniki sosai.

Ya yi kira ga masu sayar da dabbobin a ko ina suke da su sassauta wa masu saye saboda ibada za su yi.

Yusuf Hussain, Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar masu sayar da shanu ta jihar, ya ce a “wannan shekara an fi sayen Shanun layya fiye da bara.

“Akwai mutum daya da ya zo ya sayi, yan maraka guda 20 a kasuwar nan ta Kara kuma duk layya za a yi da su”, inji shi.

‘’Yan kasuwa sun koka a Legas da Ogun’
Fatake da dilallan dabobbi a jihohin Legas da Ogun na kokawa kan rashin ciniki da suka ce ya addabi kasuwancinsu a bana.

Aminiya ta zanta da ‘yan kasuwa a ziyararta ga kasuwar labar Rago, kasuwar ragunan layya mafi girma a Legas da kuma kasuwar ragunan layya mafi girma a jihar Ogun wato Karar Isheri, kan yadda al’amuran ke tafiya.

Raguna a kauswar Alabar Rago ta Legas
Alhaji Usman Bulama mai sayar da raguna, ya ce sun sayo ragunan da tsada a Arewa sun kawo kasuwannin Legas da Ogun, amma yadda ake tayawa ba ya kaiwa yadda suka sayo dabbobin.

“Mun sayo dabobbin da tsada a Arewa, mun biya kudin mota da tsada mun biya ma’aikata a kan hanya sannan mun zo nan mun iske gari ba kudi”, inji shi.

Ya ce a bara tilas ‘yan kasuwar dabobbi suka karya farashin ragunan layya, kuma hakan na iya faruwa a bana, domin babu masu saya sai daidaiku.

Malam Ibrahim Dumbul mai sayar da ragunan layya a kasuwar karar Isheri da ke mararrabar Legas da Ogun cewa ya yi “masu sauke rago cikin babbar motar tirela 10 a baya, bana da kyar suke iya sauke tirela daya zuwa biyu, saboda tsadar dabbobin a Arewa, “kuma ga shi garin ba kudi, annobar COVID-19 ta lalata komai.

“A baya masana’antu kan zo su sayi ragunan su raba wa ma’aikatansu amma yanzu ba su da halin yin haka.

“Ragon N70,000 a baya yanzu ya zama N150,000 ga shi kuma babu masu saye”, inji shi.

‘Dillalai na iya tafka asara’
Malam Yahaya Garba ya shaida wa Aminiya cewa ya shafe sama da shekara  30 yana sana’ar sayar da raguna amma bai taba ganin dabbobin sun yi tsada kamar bana ba, “ga kuma karancin masu saye, da alamu dillalai za su yi asara ne”.

“Ragon da muke sayarwa a bara N50,000 a bana N70,000 muka sayo kamarsa tun daga Arewa.

“Ga kudin mota, ko wane rago za ka kashe masa N2,000, banda kudin ma’aikata da muke kashewa a hanya.

“Ga harawa ta yi tsada, don haka nake ganin in ba Allah ne Ya kiyaye ba, za a tafka asara a kasuwar dabobbi a bana”, inji shi.

A zagayen Aminiya a kasuwannin dabobbin Legas da Ogun, kananan raguna na kaiwa N45,000 zuwa N50,000, matsakaita kuma N90,000 zuwa 120, manyan kuma daga N200,000 zuwa sama.

‘Babu turruwar sayen raguna a Kebbi’
Bana ba a samu tururuwar masaya raguna ba a jihar Kebbi, duk da babbar Sallah na kara karatowa.

Aminiya ta zanta da wani dillalin ranguna a kasuwar dabbobi ta Birnin Kebbi, Malam Auwal, wanda ya ce bana farashin raguna ya fara ne daga N35,000 zuwa N150,000.

Wani mai saye da Aminiya ta yi kicibis da shi a karar, Faruk Umar, ya ce duk da ga shi ba masu saye da yawa, amma ragunan sun yi matukar tsada.

Ya kara da cewa, ko wace shekara manyan ragunan layya uku yake saya, amma bana ba zai iya ba saboda sha’anin yau.

Ya ce babu kudi a hanun jama’a don haka zai dai duba dan madaidaici ya saya.

SOURCE:https://aminiya.dailytrust.com.ng/  

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba Yadda ake hada-hadar ragunan layya a Najeriya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?