--
An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China (Hotuna)

An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China (Hotuna)












Gwamnatin kasar China ta ce ta tabbatar da bullar wata cuta mai saurin yaduwa mai suna 'bubonic plague' wato annobar bubunic. Hakan na zuwa ne watanni bayan bullar annobar COVID-19 da aka gano a birnin Wuhan a kasar ta China.

A cewar kafar watsa labarai na Xinhua, an samu mutum daya mai cutar a yankin Mongolia kamar yadda The Cable ta ruwaito. Hukumar Lafiya ta kasar ta ce an gano cutar a jikin wani makiyayi ne a ranar Lahadi amma baya cikin hatsari kuma ana masa magani a wani asibiti kamar yadda New York Times ta ruwaito.

CNN ta kuma ruwaito cewa an garzaya da wani yaro mai shekara 15 mazaunin Ulaankhus soum zuwa wani asibiti a ranar Lahadi bayan ya ci wata dabba mai kama da bera da kare ya farauto. Hukumomi a kasar ta China sun yi gargadin mazauna kasar su dena farauta, ci ko safarar dabbobin da ka iya yada cututtuka kuma su kai rahoton duk wani dabba da suka ga ta mutu.

Wannan gargadin na hana cin dabobin zai cigaba da aiki har zuwa karshen shekarar 2020 a cewar mahukunta kasar. "A halin yanzu, akwai hatsarin yaduwar annobar a wannan garin. Ya kamata mutane su cigaba da kulawa da lafiyarsu su kuma kai rahoton duk wani ciwo da ba su gane kansa ba,"


kamar yadda China Daily ta ruwaito. Micheal Head, babban mai binciken lafiya a Jamiar Southampton ya tabbatarwa CNN cewa bullar cutar "abin damuwa ne ga mutanen da ke zama a yankin na cikin Mongolia". Ya kuma kara da cewa "ba za ta zama barazana ga duniya ba kamar yadda Covid-19 ta zama."

Wannan cutar tsohuwar annoba cewa a duniya da ta yi shekaru daruruwa da ta kashe mutane da yawa a tarihi. Sai dai, ana iya maganin ta da magungunan kashe kwayoyin hallita wato antibiotics. Wata kwayar hallita mai suna Yersinia pestis da ke zama a cikin wasu dabobi ne musamman dangin bera da kwarkwatarsu ke janyo cutar. Wasu daga cikin alamominta sun hada da zazzabi, masasara, tari da kumburin wasu sassan jiki.

SOURCE: LEGIT.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An samu bullar wata mugunyar cuta mai yaduwa a China (Hotuna) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?