LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

‘Yar madigo ta kashe budurwarta da suke iskanci tare bayan ta kama ta tana iskanci da wani

Budurwa ta mutu bayan abokiyar iskancinta da suke madigo tare ta caka mata wuka a kahon zuci ta gudu ta bar ta tsawon kwanaki a cikin daki a kulle.

Marigayiyar da aka bayyana sunanta da Vivian, ta kama budurwartan mai suna Spicykvng Vee tana lalata da wani namiji.

Spicykvng Vee, wacce tayi suna matuka a makarantarsu, taji kunya sosai bayan kamata da tayi da namiji. Sai taji tsoron kada Vivian ta bata mata suna, sai taje ta bata hakuri, ta yafe mata.

Sai dai duk da haka Spicykvng Vee tana cikin fargabar cewar Vivian za ta iya tona mata asiri a shafin Facebook, kawai sai ta dauki wuka ta caka mata a kahon zuci, inda ta gudu jihar Enugu daga jihar Delta inda tayi wannan aika-aika, bayan ta kira mahaifiyar marigayiyar ta sanar da ita cewa ‘yar ta tayi tafiya.

Gawar Vivian na cikin dakin tsawon kwana uku ba tare da kowa ya sani ba. Da farko kawayenta sun fara tunanin ko ta bata ne, amma sai aka ga kudaje suna ta yawo a cikin dakinta, sai aka kira mai gidan aka balla kofar dakin, suna shiga suka tarar da gawarta ta rube a cikin dakin.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan Spicykvng Vee ta kashe marigayiyar ta dauki talabijin da injin janareto dake gidanta ta gudu dasu jihar ta Enugu.

A karshe dai an kama Spicykvng Vee a jihar Enugu.
KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments