LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Karti 8 sun yiwa budurwa fyade a jihar AdamawaWasu karti guda takwas sun yiwa budurwa mai shekaru 33 fyade, bayan kawarta ta yaudareta ta ja ta inda mazan suke.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta sanar da kama mutane biyar daga cikin masu laifin, mutum hudu ciki hadda kawar wacce aka yiwa fyaden sun gudu.

Zainab Jafaru mai shekaru 30 a duniya ta yaudari kawarta ta kai ta inda mazan suke, inda suka yi mata fyade ita kuma ta gudu. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Suleiman Nguroje ya ce:

“A ranar 13 ga watan Yuni, 2020, an samu rahoto na cewa wasu mutane 9 sun yiwa wata budurwa fyade a Gerio, wani karamin kauye dake Jambutu, cikin karamar hukumar Yola North, jami’an ‘yan sanda da suke yankin sun kama mutane biyar daga cikinsu: Ahmadu Isma’il, mai shekatu 20; Salu Buba, mai shekaru 25; Muhammed Ali, mai shekaru 78; Abubakar Ali, mai shekaru 28; sai kuma Zainab Jafaru, mai shekaru 30.

“Lamarin ya faru a ranar 12 ga watan Yuni, 2020, a lokacin da Zainab Jafaru, ta yaudari kawarta ta rakata wani waje za ta hadu da saurayinta.

“Da zuwansu wajen, saurayin Zainab wanda yanzu muke nema, ya kira abokanan shi suka yiwa budurwar fyade daya bayan daya ba tare da amincewarta ba.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments