--
Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta shata sharuɗan buɗe makarantu

Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta shata sharuɗan buɗe makarantu



Ministan ilimi - Adamu Adamu Source: Facebook 
Gwamnatin Tarayya ta shata sharuɗa ga kafatanin makarantu da sauran cibiyoyin ilmantarwa a fadin tarayya da dole sai an cika kafin a sake buɗe su. Sharuɗan da gwamnatin tarayya ta gindaya suna kunshe ne a cikin wata takarda mai shafi 36 wanda Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya gabatar wa Majalisar Dattawa.

Takardar wadda manema labarai na jaridar The Nation suka samu damar yin hange a kanta, an yi mata lakabi da ka'idodin sake buɗe makarantu da cibiyoyin ilimi bayan rufe su saboda annobar korona. Mallam Adamu yayin gabatar da daftarin, ya sanar cewa wannan sharuɗa da aka shata su ne dabarun da za a aiwatar domin tabbatar da aminci da kuma ingancin sake buɗe makarantu.

Ya ce ganin cewa annobar korona na iya kasancewa tare da mu har zuwa wani tsawon lokaci, sharuɗan da aka shata a yanzu su na jaddada muhimmancin inganta tsarin karantarwa daga nesa.

Ministan ya yi bayanin cewa, an shata wannan sabbin sharuɗa ne tare da hadin gwiwar kwararru daga ma'aikatun lafiya, zamantakewa da kuma na ilimi. Ya ce kwararru sun jajirce wajen shimfida matakai da sharuɗan da za a kiyaye gabanin a samu amincin buɗe makarantu da sauran cibiyoyin karantarwa.

Mafi muhimmancin cikin sharuɗan da aka gindaya, shi ne sai makarantu sun ƙirƙiri wuraren killace wadanda cutar korona ta harba na wucin gadi gabanin samun cancantar buɗewa. Ya kuma zama wajibi ga duk makarantu su ƙirƙiri wata cibiyar kula da matakan dakile yaduwar cutar da za a rika kai dalibai, malamai da sauran ma'aikata yayin da suka kamu da rashin lafiya a makaranta.

Ya ci gaba da cewa, dole ne makarantu su tanadi isassun kayan aikin asibiti musamman na kare kai da kuma wuraren shan magani yadda ya dace. Kazalika ministan ya ce za a tabbatar da kiyaye dokar sanya takunkumin rufe fuska, da kuma tanadar wadatattun wuraren wanke hannu a karkashin ruwa mai gudana ko kuma sunadarin wanke hannu (sanitizer).



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta shata sharuɗan buɗe makarantu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?