--
Yanzu-yanzu: El-Rufai ya bude masallatan Juma'a da majami'u

Yanzu-yanzu: El-Rufai ya bude masallatan Juma'a da majami'u



ROHOTON: LEGIT.NG

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya sassauta dokar hana walwalar da ya kafa a jihar Kaduna - Ya bayyana cewa, masallatan Juma'a, majami'u, manyan shaguna duk za su iya budewa amma tare da kiyaye dokokin

Ya shawarci jama'ar jihar da su bada goyon baya wurin dakile yaduwar cutar duk da sassaucin da aka samu Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sassauta tsauraran dokokin da ya kafa don dakile annobar korona a jihar. Kamar yadda gwamnan ya sanar a yau Talata, 9 ga watan Yunin 2020,

ya ce manyan shaguna za su iya komawa bakin sana'o'insu. Masallatan Juma'a da Majami'u za su iya budewa a ranakun Juma'a da Lahadi kadai, amma karkashin kiyaye dokoki.

Gwamnan ya kara da bayyana cewa, masu sana'ar aski da wuraren wanke kai duk za su iya budewa. Otal za su iya budewa tare da wuraren cin abinci da kuma mashaya. Wuraren cin abincin za su iya budewa ne bayan an yi musu feshin kashe kwayoyin cuta.

Hakazalika, Gwamnan ya bayyana cewa babu yuwuwar bude makarantu da kasuwanni. "Za mu ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don samun matsaya a kan lokacin da ya kamata a bude kasuwanni ka makarantu," yace. "Shugaban ma'aikatan jihar zai sanar da lokacin da ya kamata ma'aikata su koma bakin aikinsu,

" gwamnan ya kara da cewa. Gwamna Nasir El-Rufai ya shawarci jama'ar jihar da su bada goyon baya wajen dakile yaduwar annobar a jihar. "Kamar yadda muka jure dokar hana walwala ta makonni goma, mu koma neman na kanmu ba tare da taimakawa yaduwar cutar ba.

 "Mu nuna cewa za mu iya zama lafiya duk da sassaucin dokar," El-Rufai yace. Makonni goma kenan da gwamnan ya sanar da rufe jihar tare da saka dokar hana walwala a cikinta tun bayan da ya kamu da muguwar annobar korona. Dokar dai ta hada da rufe kasuwanni, majami'u, masallatan Juma'a da na sallolin farilla biyar, shaguna da sauransu


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu-yanzu: El-Rufai ya bude masallatan Juma'a da majami'u "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?