LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu nan: Buhari ya ruguza Majalisar Shugabannin APC ta Adams Oshiomhole

Yanzu nan mu ke samun labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a sallami daukacin Majalisar NWC.

Jam'iyyar APC ta yanke wannan hukunci ne a wurin taron Majalisar NEC da ake yi yanzu haka a babban birnin tarayya.

NEC wanda ita majalisar koli a jam’iyyar ta yi na’am da shawarar da shugaban kasa ya bada, ta ruguza majalisar NWC.

Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa ya bayyana wannan mataki da jam’iyyar APC ta dauka a shafinsa na Twitter dazu.

Kamar yadda hadimin shugaban kasar ya nuna, daukacin majalisar NEC ta yi na’am da wannan mataki da aka zartar.

Bayan an ruguza majalisar NWC mai alhakin gudanar da harkokin jam’iyya, an nada wani kwamitin rikon kwarya.


Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni shi ne shugaban kwamitin rikon kwarya wanda zai rike jam’iyyar na ‘dan lokaci.

Bisa dukkan alamu, Alhaji Mai Mala Buni zai gudanar da zaben sababbin shugabannin jam’iyya watau NWC nan gaba.

Mala Buni shi ne tsohon sakataren jam’iyya na kasa, kuma tun daga lokacin da ya bar ofis, ake samun rigingimu a APC.

Da wannan mataki da aka dauka, babu wanda zai rike APC tsakanin Adams Oshiomhole, Victor Giadom da Abiola Ajimobi.

https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1276122149204475906


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments