LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda tela ya yaudari yara mata 2 da takunkumin fuska yayi musu fyadeA ranar Talata ne rundunar 'yan sandan jihar Ekiti ta gurfanar da wani Tela mai shekaru 27 mai suna Taiwo Odetunde a gaban wata kotun majistare da ke Ado-Ekiti.


An zargi telan da jan yara mata biyu masu shekaru 13 da 14 inda ya yaudaresu da alkawarin cewa zai dinka musu takunkumin fuska sannan yayi musu fyade.


'Yar sanda mai gabatar da kara, Monica Ikebuilo, ta sanar da kotun cewa wanda ake karar na fuskantar zargi a kan fyade kuma ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Yunin 2020 a Ado-Ekiti. Ikebuilo ta ce, "Wanda ake zargin ya yi wa yara kanana masu shekaru 13 da 14 fyade. Yaran kawayen juna ne kuma yayi musu alkawarin cewa zai dinka musu takunkumin fuska.


"A lokacin da yaran suka isa gidansa, ya rufe kofa tare da yin barazanar kashesu da wuka idan suka yi ihu. Ya lalata su daya bayan daya amma makwabcibsa ya kama shi a yayin da yake aikatawa.


Wannan laifin ya ci karo da sashi na biyu a layi na biyu, na dokokin hana cin zarafin jinsi na jihar Ekiti na 2019." Ikebuilo ta yi kira ga kotun da ta tsare mai laifin a gidan gyaran hali kafin ta samu shawara daga ofishin daraktan gurfanarwa.


Kotun bata saurari rokon wanda ake zargin ba. Mai shari'a Adefumike Anoma, ta bada umarnin ajiye wanda ake zargin a gidan gyaran hali har zuwa ranar 27 ga watan Yulin 2020.


A wani labari makamanccin wannan, mun ji cewa undunar 'yan sandan jihar Bauchi ta damke Yusuf Saleh mai shekaru 36 sakamakon zarginsa da ake da yin luwadi sa kaninsa. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ahmed Wakili, wanda ya bayyana hakan a wata takarda, ya ce an kai musu rahoton al'amarin a ranar 5 ga watan Afirilun 2020.


Kuma mahaifin yaran ne ya kai rahoton. Ya ce Saleh ya ja kaninsa zuwa wani kango inda ya yi lalata da shi ta baya. DSP Wakili ya kara da cewa, wanda ake zargin ya siyawa wanda ya lalata biskita da lemun kwalba don toshe masa baki.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments