LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda mutanen gari da 'yan sintiri suka kashe 'yan ta'adda 5 a Katsina

'Yan sintiri na unguwa a ranar Juma'a da rana sun kashe wasu bata gari biyar da ake zargin 'yan bindiga ne a garin Wagini da ke karamar hukumar Batsari na jihar Katsina. HumAngle ta ruwaito cewa 'yan sintirin sun yi galaba a kan 'yan bindigan hakan yasa suka yi nasarar kashe biyar yayin da wasu uku suka tsere a cikin cinkoson jama'a.

Yasir, wani mazaunin garin ya ce, "Sun shigo kasuwar garin mu misalin karfe 2.30 na rana bayan sallar Juma'a a yau. Ana zargin sun neman wanda za su sace suyi garkuwa da shi don samun kudin fansa ne. "Yan sintirin sun gane 'yan ta'addan a kasuwar, sun yi yunkurin tserewa amma 'yan sintirin da taimakon mutanen gari sun fi karfinsu inda suka kashe biyar cikinsu."

Bata garin sun kai hari a garin a ranar 25 ga watan Yunin 2020 misalin karfe 11 na dare inda suka kashe mutum biyu tare da raunata wasu da dama. Sun kuma bannatar da dukiyoyin al'umma, " in ji shi. "Bata garin sun kai hari a garin Kurmiyal da Wagini misalin karfe 11 na dare, sun harbe mutum biyu har lahira,

wasu da dama sun jikkata kuma sun sace Haruna Aj da Mani Allera mazauna kauyen Kurmiyal. "Ba su tuntubi kowa ba kuma babu wani jami'in hukumar tsaro da ya zo garin mu bayan afkuwar lamarin,"

a cewar Yasir. Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa sojoji da 'yan sanda sun koma cikin garuruwa saboda tsoron harin ramuwar gayya. Musa, wani mazaunin garin da aka gani yana kwashe kayansa ya ce, "babu wanda zai hana su kawo mana hari, na tabbatar da hakan. Za su dawo daukan fansa kuma ba za tayi kyau ba."

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments