LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Wata Wakiliya A Majalisar Wakilan Amurka Musulma Ta Yi Allawadai Da TrumpIlham Umar wakiliya a majalisar wakilan kasar Amurka
Ilham Umar wakiliya a majalisar wakilan kasar Amurka ta suki shugaban kasar ta Amurka Donal Trump kan yadda yake rikon sakainan kasha da batun cutar korona a kasar.


Kamfanin dillancin labaran “Jawan” na kasar Iran ya nakalto Umar tana fadar haka a yau Lahadi, ta kuma kara da cewa shugaban kasar yana tsammani da sakonnnin da yake rubutawa a shafuffukansa na Twitter ne zai gudanar da harkokin kasar.Ilhan Umar dai ita ce wakiliya musulma da aka fara zaba zuwa majalisar wakilan kasar ta AMurka. Kuma ta dade tana sukan yadda shugaban yake gudanar da harkokin tafiyar da kasar.Ya zuwa yanzu dai cutar Korona ta kama mutane kimani 2,330,000 tun lokacin bullatar a kasar a cikin watan Maris da ya gabata, sannan mutane akalla 120, 000 daga cikinsu dun rasa rayukansu.Har’ila yau kissan wani bakar fata a ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata ya tunzura mutanen kasar ta Amurka fitowa zanga-zangar yin allawadai da tsarin wariya, sannan suna bukaci a kawo sauyi a wannan tsarin wanda ya dade yana cinye rayukan bakar fata a kasar.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments