LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Jakadan Kasar Iran A Venezuela Ya Ce Jirgin Ruwan Kasarsa Na Shida Ya Kusan Isa Kasar Ta Venezuela

Jakadan kasar Iran a birnin Caracas na kasar Venezuela ya bada sanarwan cewa jirgin ruwan kasar Iran na shida dauke da kayakin abinci ya kusan isa kasar ta Venezuela.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya nakalto Hujjatullahi Sultani jakadan Iran a Venezuela ya na fadar haka a lokacinda ya ke hira da tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon.

Sultani ya kara da cewa jirgin ya bar tashar jiragen ruwa na “Shaheed Raja’ii da ke kudancin kasar ta Iran ne, tun ranar 17 ga watan Mayu na wannan shekara dauke da abinci zuwa kasar ta Venezuela, wacce take fama da takunkuman tattalin arziki wadanda gwamnatin kasar Amurka ta dora mata.

Tun cikin watan Afrilu na wannan shekara, ya zuwa yanzu kasar Iran ta aike da jiragen ruwa 5 dauke da man fetur lita miliyon 1.5 zuwa kasar Venezuela don kawo karshen karancinsa a kasar wanda takunkuman Amurka suka jawa.

Gwamnatin kasar Amurka dai tana son kifar da gwamnatin shugaba Nicolas Maduro na Venezuela tun farkon shekara ta 2019, amma ta kasa yin hakan har zuwa yanzu.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments