--
Wata sabuwa: Trump na yunkurin tafka magudin zabe – Joe Biden

Wata sabuwa: Trump na yunkurin tafka magudin zabe – Joe Biden

Dan takarar shugaban kasar Amurka a babbar jam’iyyar adawa ta Democrat, Joe Biden na zargin shugaba Donal Trump na kasar ta Amurka da kokarin tafka magudi ta hanyar satar kuri’u, a babban zaben shugaban kasar da za a gabatar a ranar 3 ga watan Nuwambar shekarar nan ta 2020.

Joe Biden wanda yake tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, ya bayyana hakane a wata hira da yayi da gidan talabijin akan zaben da za’a gabatar a kasar nan da watanni biyar masu zuwa.

Biden ya ce: “Babban abinda nake fargaba a wannan zaben mai gabatowa shine, wannan shugaban kasar tamu na yanzu ka iya tafka magudi ta hanyar satar kuri’u.”

Ya kara da cewa: “Wannan mutumin ya gama shirya zaben fitar da dan takara a cikin takarda a lokacin da yake zaune a cikin ofishinsa, wannan ya tabbatar da zabe ne na zamba wanda yake a bayyane.

Joe Biden ya ce matukar Donald Trump ya fadi zabe kuma yaki yadda ya fita daga fadar shugaban kasa to tabbas sojoji ne za su fitar da shi daga fadar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Wata sabuwa: Trump na yunkurin tafka magudin zabe – Joe Biden"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?