--
An kashe Likita, an ƙone gawarsa ƙurmus a jihar Zamfara

An kashe Likita, an ƙone gawarsa ƙurmus a jihar Zamfara

ROHOTON: LEGIT.NG

Mun samu cewa, wasu mahara wadanda ba a san ko su wanene ba, sun aikata wani mummunan ta'addanci kan ma'aikacin kiwon lafiya a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, ta bayyana cewa ta fara bincike kan mutuwar wani Likita, Enoch Okpara, wanda wasu mahara suka kashe kuma suka ƙone gawarsa.

Marigayi Okpara a yayin rayuwarsa, ya kasance kwararren Likitan mata wanda ma'aikaci ne a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke birnin Gusau. An tsinto gawar Likitan ne a ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, a cikin gidansa da ke Unguwar Mareri ta birnin Gusau.

Shehu Muhammad, jami'in hulda da al'umma na hukumar 'yan sandan jihar, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Lahadi.

Ya ce, kwamishinan 'yan sanda na jihar, Usman Nagogo, ya ba da umarnin a gudanar da binciken diddigi domin bankado miyagun da suka aikata wannan mummunar ta'asa. "Mun samu rahoto na bakin ciki game da kisan gillar da aka yi wa wani likita,

Enoch Okpara da Yammacin ranar Asabar," in ji shi. "Saboda mummunan yanayin kisan, Kwamishinan 'yan sanda, Mista Usman Nagogo, ya ba da umarnin a fara bincike kan lamarin." Da yake tsokaci kan lamarin, Mannir Bature, mataimakin shugaban kungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar, ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai nutsuwar gaske.

Ya ce an nemi likitan an rasa ne yayin da bai fito wurin bauta ba kamar yadda ya saba a duk safiyar Asabar. Hakan ya sa aka tuntubi wasu daga cikin abokan aikin Okpara, inda aka yi ta gwada kiran lambar wayar sa ta hannu ba tare da ya amsa ba, lamarin da ya sanya aka yanke hukuncin ba kalau ba.

Yayin da abokan aikinsa suka binciki gidan da marigayin ya ke zaune shi kadai, an ga motarsa ​​a ajiye a harabar gidan, hakan ya sa aka gaggauta neman 'yan sanda su shiga lamarin. A cewar Bature, an gano ƙonanniyar gawar mamacin a farfajiyar gidansa yayin da bangon dakin da ya ke kwana ya kasance jina-jina da jini.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An kashe Likita, an ƙone gawarsa ƙurmus a jihar Zamfara"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?