--
Wata Sabuwa: Sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo ya tada kura a PDP

Wata Sabuwa: Sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo ya tada kura a PDP



Sauya shekar mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi zuwa jam'iyyar PDP ya sa wasu daga cikin manema tikitin jam'iyyar don takara ke korafi a kan yadda ake bai wa masu sauya sheka fifiko a jam'iyyar.

A kalla 'yan takara takwas ne suka siya fam don nuna ra'ayin fitowa neman kujerar gwamnan jihar, ciki kuwa har da Eyitayo Jegede (SAN). Majiya mai karfi ta ce 'yan takarar na zargin mataimakin gwamnan da nada shugaban kwamiti tare da mambobin kwamitin zaben fidda gwani a jihar.


Wata majiya ta ce Ajayi da kansa ya biya wani jirgi guda don dauko kwamitin gudanar da ayyuka na jam'iyyar PDP wanda ya samu jagorancin Prince Uche Secondus don karbarsa zuwa jam'iyyar a yau.


Har zuwa daren jiya Lahadi ba a tabbatar da zargin ba. Daya daga cikin wadanda suka siya fam din kuma ya ki yin mubaya'a ya bayyana komawar Ajayi jam'iyyar PDP da ci gaba amma ccewa jam'iyyar za ta rikice matukar Ajayi ya samu yadda ake yadawa.

Dan takarar ya ce: "Ta yaya zai zo yanzun nan jam'iyyar sannan ya nemi nada shugaba da mambobin kwamitin zaben fidda gwani shi kadai? Ko saboda hakan ne ya yi hayar jirgi don ya kawo mambobin NWC don tarbarsa?

Wannan cin mutunci ne. "Mu zuba ido mu ga abinda zai faru amma su sani, mu ba sakarkaru bane a wannan jam'iyyar," Amma a takardar da kakakin Ajayi, Babatope Okeowo ya fitar, ya musanta cewa shi NWC ta fitar a matsayin dan takararta.

Ya ce tsegumi da rade-radi basu damunsa. Ajayi baya ta masu neman bata masa suna ta hanyar haddasa gaba tsakaninsa da 'yan PDP. A baya Legit.ng ta kawo cewa mataimakin gwamnan jihar Ondo, Hon. Agboola Ajayi, ya sauya sheka daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Agboola ya sanar da barinsa jam'iyyar mai mulki a ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni, jaridar Leadership ta ruwaito. Agboola wanda ya sanya hannu a takardar barinsa jam’iyya mai mulki a Ward 2, Apoi Na karamar hukumar Ese-Odo da ke jihar, ya gaggauta daukar takardar zama dan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Wata Sabuwa: Sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo ya tada kura a PDP "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?