--
Wata sabuwa: Gwamnatin Tarayya za ta sa haraji a kan irinsu Facebook da Netflix

Wata sabuwa: Gwamnatin Tarayya za ta sa haraji a kan irinsu Facebook da Netflix

ROHOTON: LEGIT.NG

Gwamnatin Najeriya za ta rika karbar haraji a kan wasu kamfanonin waje - Irinsu Facebook da Twitter za su rika biyan haraji na kudin da su ka samu Wadannan kamfanoni su na samun kudi a Najeriya ta hanyar talla da bidiyo A ranar Litimin, 8 ga watan Yuni, 2020 aka fitar da rahoto cewa ana kokarin sa haraji ga kamfanonin sada zumunta da yanar gizo da su ke aiki, su na samun kudi da Najeriya.

Gwamnatin tarayya Najeriya za ta shigo da haraji ne kan kamfanoni da ke da shafukan wallafa bidiyo, da na kallo da kuma masu dandalin sada zumunta da ke yin kudi da ‘yan kasar. A shekarar nan ne Ministar tattalin arziki, Zainab Ahmed ta kawo wata dokar haraji wanda ta yi wa dokar kudi ta 2019 garambawul domin Najeriya ta samu damar tatsar kamfanonin.

Ministar kudin ta kawo wannan doka ne da nufin daurawa wadannan kamfanoni na zamani haraji na abin da su ka samu, za a rika biyan wannan haraji ne ga hukumar FIRS.
Ministar kudi Hoto: Facebook/Zainab Shamsuna Ahmed Source: Instagram 

Netflix, Facebook, da Twitter, su na cikin kamfanonin waje da su ke da shafukan wallafa bidiyo da na kallo da kuma tallata hajjoji a Najeriya, hakan na nufin su na samun kudi a kasar. Sauran kamfanoni irinsu Alibaba da kuma Amazon su na samun kudi a Najeriya ne ta hanyar karbar bayanai wurin ‘yan kasar domin shigo masu da kayan da su ka saya daga ketare.

Jaridar Punch ta ce wannan dokar da aka kawo za ta yi aiki ne kan duk wani kamfanin ketare da ya ke samun kudin shiga na akalla Naira miliyan 25 a Najeriya a cikin shekara guda. Sannan kuma gwamnati za ta rika karbar haraji a kan kamfanonin da ke amfani da shafukan yanar gizo masu ajin (.ng).

Za a rika karbar wannan haraji ne sau guda duk shekara. Rahoton ya ce za a saukake wannan doka a kan kudin da aka samu da ‘yan kasar wajen da ke zaune a Najeriya, da kuma hidimar da aka yi ga hukumomi da kuma makarantun ilmi.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Wata sabuwa: Gwamnatin Tarayya za ta sa haraji a kan irinsu Facebook da Netflix "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?