LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Tashin hankali: Miji ya kashe matarsa ya jefa gawar cikin rijiya a KatsinaRundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wani mutumi dan shekara 40 mai suna Abdulrahman Abdulkarim, da laifin kashe matarsa mai shekaru 19 mai suna Wasila Sada, sannan ya jefa gawarta cikin rijiya.

Mutumin wanda yayi magana da manema labarai a jiya Alhamis 25 ga watan Yuni, an ruwaito cewa ya aikata laifin a kauyen Madabu-Dabawa dake karamar hukumar Dutsinma cikin jihar Katsina.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isa ya ce:

“A ranar 14 ga watan Yuni, 2020, da misalin karfe biyu, mun samu kiran waya cewa wani mai suna Abdulrahman Abdulkarim mai shekaru 40 daga kauyen Madabu-Dabawa, cikin karamar hukumar Dutsinma dake jihar Katsina, ya kashe matarsa mai suna Wasila Sada, mai shekaru 19 a duniya, sannan ya jefa gawarta cikin rijiya.

“DPO na Dutsinma ya jagoranci jami’an ‘yan sanda zuwa inda lamarin ya faru, sun fito da gawar inda suka kai ta asibiti, inda aka tabbatar da cewa ta mutu bayan gabatar da gwaje-gwaje.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments