LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Shehnaz Laghari: Mace ta farko Musulma da ta fara tukin jirgin sama sanye da NiqabMun ga labarai da dama da ake daukar Hijabi a matsayin ci baya da rashin wayewa, sannan ake yiwa mata Musulmai kallon marasa wayewa a duniya.

To sai dai akwai labarai da dama dake nuni da yadda mata masu sanya Hijabi suka yi abubuwa na ban mamaki da ba a taba tunanin za suyi ba, wannan labarin yana daya daga cikinsu. Wannan labarin wata Musulma ce ‘yar kasar Pakistan.

Mace ce mai son taimakon al’umma sannan kuma ‘yar siyasa. Ta zama daya daga cikin mata abin koyi wajen kawo cigaba a kasar Pakistan. Ta samawa mata da yara ‘yan ci a Pakistan.

Tana da ‘ya’ya guda uku. Kyaftin Shehnaz Laghari, tana aiki tukuru wajen ganin an samu daidaito wajen yara mata da ake ganin basu da cigaba a cikin kasar Pakistan.

Kyaftin Shehnaz Laghari ita ce mace ta farko a kasar Pakistan da ta fara tukin jirgin sama sanye da Hijabi da Niqab. Sanadiyyar wannan nasara da ta samu ya sanya aka sanya sunanta a cikin littafin wadanda suka samu nasara a duniya na Guinness Book.

Ita ka dai ce mace ta farko da ta fito daga kasar Pakistan da sunanta ya shiga cikin wannan littafi. Hakan na nuni da cewa idan mutum ya sanya kanshi komai mai yiwuwa ne.

Har ila yau, ma’aikaciya ce a cikin al’umma, kuma tana da cibiyoyi na horar da mata da karfafa musu guiwa a kasar Pakistan. Tana yiwa matan kasar Pakistan Hidima ta hanyar bude cibiyoyin karatu da wuraren koyon dinki kyauta ga mata talakawa.

Ta fada harkar siyasa a matsayin shugaba mai zaman kanta a babban zaben da aka gabatar a Lahore a shekarar 2013, amma ba ta samu nasara ba. A cewar kafafen yada labarai na Lahore, Shahnaz ta shiga jam’iyyar Pakistan Muslim League-Quaid (PMLQ) a watan Mayun 2018.

Kasar Pakistan dai ana yi mata kallon kasa da maza suke da rinjaye, inda ita kuma Kyaftin Shehnaz Laghari ta karya wannan alkadari na su.

Wannan babbar nasara ce ga mace, kamar yadda ake ganin al’adar kasar Pakistan maza sune masu rinjaye, inda ake hana mata shiga wasu al’amura da yawa a kasar.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments