--
Satar kaji: Kotu ta daure saurayi da budurwarsa

Satar kaji: Kotu ta daure saurayi da budurwarsa



ROHOTON:LEGIT.NG

Wata kotun majistare da ke zama a Kafanchan a jihar Kaduna ta daure wani matashi mai shekaru 35 mai suna Abdullahi Sani tare da budurwarsa mai shekaru 20 bayan kama su da tayi da laifin sata,

Sarah Paul da Abdullahi sun saci kaji 64 wadanda suka dinga yanka wa.

Jami'a mai shigar da kara ta bayyana cewa ana tuhumar su da hadin baki wurin aikata laifin na sata. Hakan ya ci karo da sashi na 58, 332, 270 da 312 na dokokin Penal Code na jihar Kaduna.

Yayin karanto hukuncin, Alkali Michael Bawa, ya yanke wa Abdullahi Sani hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon wata 38. Ita kuwa Sarah ta samu hukunci wata 13 saboda rawar da ta taka wajen aikata laifin.

Alkalin ya kara da cin tarar Abdullahi N600,000 yayin da Sarah za ta biya N200,000 a matsayin diyya, jaridar Aminiya ta Daily trust ta ruwaito.

Da farkon shari'ar, mai shigar da kara Sifeta Esther Bishen ta sanar da kotu cewa wata mai suna Hilary Garba ta kawo korafi gaban hukumar 'yan sanda.

Ta ce, a ranar 21 ga watan Mayun 2020 ne aka fasa mata gida cikin dare tare da sace mata kajin gidan goma masu kwai da kudinsu ya kai N781,970.

Ta ce an kama Sarah Paul yayin da take soya wasu daga cikin kajin.

Ta ce, 'yan sandan sun gano wayoyin hannu, talabijin, janareto, katifu, injin amplifier da dardumar daki wadanda ake zargin na sata ne.

Ta roki kotun da ta hukunta su bisa tanade-tanaden sashi na 125 sakin layi na takwas na kundin manyan laifuka.

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da samar da 'yan sandan sa kai wadanda za su dinga aiki a karkashin kulawar jami'an 'yan sandan Najeriya da ke jihar.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa, a wata takarda da mai bada shawara ta musamman ga Matawalle a kan yada labarai, Zailani Bappa ya fitar, ya ce sabuwar cibiyar tsaron za ta tattara 'yan sa kai daga kananan hukumomi 14 na fadin jihar.

Kamar yadda Bappa ya bayyana, za a horar da 'yan sa kan ne a hukumar 'yan sandan Najeriya.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Satar kaji: Kotu ta daure saurayi da budurwarsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?