--
Rikicin kabilanci: Hakimi, Limami tare da wasu mutum 3 sun rasu

Rikicin kabilanci: Hakimi, Limami tare da wasu mutum 3 sun rasu



ROHOTON: LEGIT.NG

Hakimin kauyen Bagoni da limamin garin, duk sun mutu sakamakon harin tsakar dare da 'yan tawaye suka kai musu a jihar Taraba. Mutum uku sun riga mu gidan gaskiya a kauyen Wurbo da ke karamar hukumar Bali ta jihar Taraba. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane da dama sun rasa rayukansu a ranar Juma'a a kauyen Tunga sakamakon harin ba-zata da 'yan ta'adda suka kai musu.

Kauyukan da aka kai wa hari duk na Jibawa ne; wani sassa na kabilar Jukun. A yayin harin, an kone gidaje tare da dukiyoyin miliyoyin Naira da suka hada da amfanin gona wanda maharan suka yi awon gaba da su. Wani mazaunin kauyen Bagoni wanda ya tsallake rijiya da baya ya ce, Jibawa basu daga cikin rikicin da ke aukuwa tsakanin 'yan kabilar Tiv da Jukun a jihar.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, sakamakon harin da aka kai wa Jibawa a Bali, rikicin ya shafi yankin jihar na tsakiya kenan. An gano cewa, matasan Jibawa na shirye-shiryen mayar da martani a kan kauyukan Tiv, lamarin da yasa 'yan kabilar Tiv ke tserewa daga kauyukansu.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, an nakasa noma a yankin don a yanzu babu mai zuwa gona sakamakon tsoron harin 'yan tawayen. Har a halin yanzu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP David ya ce yana jiran bayani game da harin. Amma kuma, tuni aka kira taron gaggawa na jami'an tsaro a gidan gwamnatin jihar da ke Jalingo a ranar Asabar. Taron wanda ake yin sa na sirri,

ya samu halartar manyan jami'an tsaro na cibiyoyi daban-daban da suka hada da 'yan sanda da soji. A wani labari na daban, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya sanar da mutuwar Remi Omotoso, daya daga cikin mambobin kwamitin yaki da cutar korona kuma tsohon shugaban Standard Chartered Bank. A wata takardar da Yinka Oyebode, sakataren yada labarai na Fayemi ya fitar, ya ce Omotoso ya rasu a ranar Juma'a bayan gajeriyar rashin lafiya. Ya rasu yana da shekaru 75 cif a duniya.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Rikicin kabilanci: Hakimi, Limami tare da wasu mutum 3 sun rasu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?