--
Rashin daidaito a alkalumman NCDC: El-Rufai ya tona asirin wasu gwamnoni

Rashin daidaito a alkalumman NCDC: El-Rufai ya tona asirin wasu gwamnoni



ROHOTON: LEGIT.NG

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ya ce NCDC na wasa da hankalin mutane a kan yawan masu korona Bawan Allah mai suna Jibrin Ibrahim ya tabbatar da cewa wasu daga cikin gwamnonin jihohi ba su da gaskiya don samfur kadan suke tura wa NCDC - A martanin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce akwai kamshin gaskiya a zancen Gwamnan jihar Kaduna,

Malam Nasir El-Rufai ya yi martani a kan zargin wasu gwamnonin jihohi da ake yi da tura wa hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) da ake da samfur amma suna rage yawan masu cutar. Gwamnan ya ce akwai kamshin gaskiya a wannan ikirarin. Gwamnan ya yi martanin nan ne a daya daga cikin wallafar Jibrin Ibrahim, a shafin twitter. Ya zargi rashin gaskiya a alkalumman NCDC na masu cutar da take fitarwa a kowanne yammaci.

Ibrahim ya zargi wasu gwamnonin inda suke tura samfur kadan ga NCDC don rage yawan masu cutar korona a jihar don dawowar al'amuran walwala a jihohin. "Wasan lambobi na kowanne yammaci da NCDC ke saki. Me kuke tunani? Ana karbar samfur ne daga dakunan gwaji na kowacce jiha wanda gwamnan jihar ke kula da shi. "Wanda ke kula da samfur kuwa shi zai iya juya lambobin. Gwamnonin na son kananan lambobi," ya wallafa.

A kan wannan wallafar, gwamnan jihar Kaduna ya yi martanin cewa ba dukkan gwamnonin ke yin haka ba. Kamar yadda yace, babban birnin tarayya, Kaduna da Legas na kokarin bankado dukkan masu cutar. Ya wallafa: "Akwai kamshin gaskiya a wannan zancen. Amma ba dukkan jihohi ke fitar da lambobi kadan ba. Babban birnin tarayya, Kaduna da Legas duk suna kokarin fitar da masu cutar saboda muna son dakile cutar.

"Muna son tseratar da rayukan jama'armu. Bamu son samun mace-macen da basu da bayani gamsasshe." Wata ma'abociyar amfani da twitter ta ce bata gane kan lambobin da ke fitowa daga yankin kudu maso gabas. Ta ce jihohin Legas, Kaduna da FCT kadai ta aminta da alkalummansu.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Rashin daidaito a alkalumman NCDC: El-Rufai ya tona asirin wasu gwamnoni "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?