--

Ni ba Musulmi bane, amma na san Annabi Muhammad shine mutumin da yafi kowa a duniya – Chicharit

Ni ba Musulmi bane, amma na san Annabi Muhammad shine mutumin da yafi kowa a duniya – Chicharit

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Javier Hernandez Balcazar ya nuna soyayyar shi ga Annabi Muhammadu (SAW). “Ni ba Musulmi bane, amma na san cewa mutumin da yafi kowa a duniya shine Annabi Muhammad (SAW),” cewar Balcazar wanda aka fi sani da Chicharito.

Chicharito dai shine dan wasan kasar Mexico na farko da ya fara buga kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United. Ya buga wasan gasar kwallon kafa ta duniya a shekarar 2010 sannan kuma ya buga wasan CONCACAF a shekarar 2011, inda ya zama dan wasan da yafi kowanne cin kwallo a lokacin kuma aka bayyana shi a matsayin dan wasan da yafi kowanne tsada a wannan gasa.

Annabi Muhammadu (SAW) dai ya zama daya daga cikin wadanda yawancin kungiyoyi a kasar Amurka, yankin Turai da kuma Asia, suke kaiwa hari a koda yaushe. Annabi Muhammad (SAW), shine mutumin da Allah da kanshi ya kira sunayen shi da dama a cikin Qur’ani.

“Kuma waɗanda suka yi ĩmani, suka aikata ayyukan ƙwarai, sannan suka yi ĩmani da abinda aka saukar a kan Muhammad – suka gaskata cewa gaskiya ne daga Ubangijinsu – (Allah) zai kankare musu miyãgun ayyukansu, kuma Yã kyautata hãlãyensu” [Suarh Muhammad 47: Ayah 2].

Koma dai yaya ne, furcin dan wasan Javier Hernandez Balcazar misali ne na girmamawa ga mahangar mabiya wani addini daban. kwarai kuwa, ya kamata mu girmama wasu game da addininsu.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Ni ba Musulmi bane, amma na san Annabi Muhammad shine mutumin da yafi kowa a duniya – Chicharit"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?