--
Hotuna: Matashi dan Najeriya ya kera Keke Napep mai amfani da hasken rana a cikin kwanaki 21

Hotuna: Matashi dan Najeriya ya kera Keke Napep mai amfani da hasken rana a cikin kwanaki 21



Anthony Obinna Okafor yana daya daga cikin ‘yan Najeriyan da basu bari halin da kasar ta shiga a yanzu ya hana su ganin sun cimma burinsu ba.

Matashin saurayin da ya kammala jami’ar Nnamdi Azikiwe a fannin kere-kere na zamani, yana so a dinga kiranshi da suna Elon Musk din Afrika.

“Ina so na zama mutumin da yake kera motoci masu amfani da hasken rana a Afrika kamar dai yadda Elon Musk yake yi a kamfanin shi na Tesla,” cewar shi.

Abin da ya kera na farko a yanzu shine Keke Napep mai amfani da hasken rana, wanda ya kaddamar dashi a garin Abakaliki, jihar Ebonyi.

A wata hira da yayi da jaridar Vanguard, Okafor ya bayyana cewa ya shafe kimanin makonni uku yana aikin kera wannan keke napep mai amfani da hasken rana. A cewar shi hakan ya samo asali ne saboda rashin kayan aiki.

Ya ce ya samu hadin guiwar makarantar koyar da sana’o’i ta Ebonyi, inda yace ba abu bane mai sauki ba a gareshi kammala wannan keke napep.

Da yake magana akan yadda keken yake aiki, Okafor ya ce ana yi masa caji ne da hasken rana. Sannan kuma ana iya yi masa caji da wutar lantarki ko janareto.

“Idan anyi masa caji sosai, yana iya tafiyar kilomita 60 zuwa 70. Idan kuma akwai rana sosai yana iya kara tafiyar kilomita 10,” ya ce.

Matashin saurayin ya ce har yanzu bai da masaniya akan sunan da zai sanyawa wannan keke nashi, amma yana tunanin ya sanya masa suna Okafor, kamar dai yadda Ford, Toyota, Honda, Bajaj duka sunayen wadanda suka yi su ne.

Ya ce idan har ya samu damar haduwa da shugaba Buhari zai tambayeshi jari ne da zai cigaba da wannan aiki na shi.

Okafor ya ce wasu daga cikin kayan da ya hada wannan keke nashi da su duka an shigo dasu daga kasar waje ne. Ya kara da cewa yana da tabbacin irin wadannan abubuwa duka zai iya kera su a Najeriya idan har ya samu isashen kudi.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Hotuna: Matashi dan Najeriya ya kera Keke Napep mai amfani da hasken rana a cikin kwanaki 21"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?