--
Macen Macen Kano: Kashi 15% ne kadai suke da alaka da cutar korona - Ganduje

Macen Macen Kano: Kashi 15% ne kadai suke da alaka da cutar korona - Ganduje

ROHOTON: LEGIT.NG

Gwamnatin Kano ta ki gamsuwa da rahoton da gwamnatin tarayya ta fitar na cewa sama da kashi 50 cikin 100 na kusan mutum 1,000 da suka mutu a watan Afrilu na da alaƙa da cutar korona.


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce yana ja da binciken mace-macen da Gwamnatin Tarayya ta yi wanda ya nuna cutar korona ce ta yi ajalin fiye da kashi 50 da aka samu a jiharsa. Jaridar Punch ta ruwaito Ministan Lafiya Osagie Ehanire yana cewa,


adadin mutane 979 ne suka mutu cikin makonni biyar a jihar Kano sakamakon kamuwa da cutar korona. Ministan ya yi furucin hakan ne a yayin zaman tattaunawa da kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona da aka gudanar cikin babban birnin kasar na tarayya. 

Rahoton kwamitin yaki da cutar korona da gwamnatin Kano ta kafa ya ce kashi 15 cikin 100 na mamatan da suka mutu ya ta'allaka ne sakamakon kamuwa da cutar covid-19. Wannan rahoto da fadar gwamnatin Kano ta fitar a ranar Talata na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan da Ministan Lafiya ya gabatar da na kwamitin Gwamnatin Tarayya PTF. 

Jagoran kwamitin na Jihar Kano, Farfesa Mukhtar Gadanya na Asibitin koyarwa na Mallam Aminu, ya ce mutum 255 ne kacal a cikin mamata 1,774 suka rasu sakamakon cutar korona. A yayin karbar rahoton binciken da aka gudanar, 


Ganduje ya yabi kwazon da kwamitin ya yi, wanda ya ce yana kunshe da alkaluma masu gamsarwa da saukin fahimta. Gwamnan ya kara da cewa shi da kansa zai mika wannan sakamako zuwa fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya kawar da shakkun masu tantama a kai. 


Jagoran kwamitin masu bincike na Kano ya ce kashi 70 na mutanen da ajali ya katsewa hanzari sun mutu ne a sakamakon wasu cututtukan kamar hawan jini da ciwon suga. 

Ya kuma ce kashi 76 cikin mutanen da suka kwanta dama sun kasance dattawa ‘yan shekara 50 zuwa sama. Ya kara da cewa mutum 1,774 ne suka rasu daga ranar 1 ga watan Afrilu zuwa 2 ga watan Mayu, 2020 a kananan hukumomi takwas da ke kwayar birnin Kano. 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657



0 Response to "Macen Macen Kano: Kashi 15% ne kadai suke da alaka da cutar korona - Ganduje"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?