--
Ma’aikatar Ayyukan Leken Asiri Ta Kasar Iran Ta Yi Karin Bayani Kan Ba’amurken Da Ta Saki

Ma’aikatar Ayyukan Leken Asiri Ta Kasar Iran Ta Yi Karin Bayani Kan Ba’amurken Da Ta Saki



Shugaban sashin yake da ayyukan liken asiri a ma’aikatar liken asiri na kasar Iran ya yi karin bayani kan yadda aka yi ma’aikatar ta sallami wani ba’amerike mai suna Michael White wanda yake zaman kaso saboda ayyukan liken asiri wa kasar Amurka.

(ROHOTON: ABNA24.com) Shugaban sashin yake da ayyukan liken asiri a ma’aikatar liken asiri na kasar Iran ya yi karin bayani kan yadda aka yi ma’aikatar ta sallami wani ba’amerike mai suna Michael White wanda yake zaman kaso saboda ayyukan liken asiri wa kasar Amurka.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta nakalto shugaban sashen yana cewa Michael White ya cinye wani bangare na hukuncin da aka yanke masa na zaman gidan kaso, don haka ma’aikatar ta tausaya masa saboda rashin lafiyan da yake fama da ita da kuma halaye masu kyau da ya nuna a lokacin da yake daure a nan Iran, inda ya yanke shawarar sakinsa.

Ma’aikatar ta ce an sake shi ba tare da wata tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ba.

An kama Michael White ne bayan ya shigo kasar Iran da sunan dan yawon bude ido, amma jami’an tsaro a ma’aikatar liken asirin kasar suka bi shi har suka gano manufarsa ta shigowa kasar, wato yi wa gwamnatin Amurka liken asiri.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Ma’aikatar Ayyukan Leken Asiri Ta Kasar Iran Ta Yi Karin Bayani Kan Ba’amurken Da Ta Saki"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?