--
Kano:Ganduje ya bada umarnin yi wa masu mukami a gwamnatinsa gwajin miyagun kwayoyi

Kano:Ganduje ya bada umarnin yi wa masu mukami a gwamnatinsa gwajin miyagun kwayoyi

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ana shirin yi wa duk masu rike da mukaman siyasa, ma'aikatan gwamnati da dalibai gwajin dole na miyagun kwayoyi a jihar. A wata takarda da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, ya fitar ranar Juma'a ya sanar da hakan. A yayin jawabi a ranar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi na duniya,

Garba ya ce za a fara gwajin dole daga cibiyar kula da magunguna. Gwamnatin Ganduje na kokarin gani ta yaki safara tare da ta'ammali da miyagun kwayoyi. Saboda haka ne ta kafa kwamitin yaki da hakan a jihar. "Gwamnan ya samar da shirye-shirye da za su tabbatar da an shawo kan matasalar amfani da miyagun kwayoyi.


"Wannan ya hada da kafa kwamitin yaki da hakan wanda yake kamawa tare da kwace miyagun kwayoyin miliyoyin naira," yace. Ya yi kira ga jama'a da a dage wurin wayar da kan matasa a kafafen sada zumuntar zamani don su gane hadurran da ke tattare da ta'ammali da miyagun kwayoyi. Su gane cewa hakan na da matukar hatsari ga rayuwarsu tare da tattalin arzikin kasar nan baki daya.

Kamfanin Dillancin Labarai ya ruwaito cewa, majalisar dinkin duniya ta ware ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da ta'ammali da miyagu kwayoyi da safararsu a fadin duniya. An ware ta ne don bayyana kokarinta wurin cimma manufar al'umma na yakar ta'ammali da miyagun kwayoyi. A wannan ranar ta shekarar nan, ana kokari wurin wayar da kai tare da ilmantar da jama'a don su gane matsalolin kwayoyi ga al'umma baki daya.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sanda babban birnin tarayya da ke Abuja ta damke wasu mutum 24 da ake zargin su da laifukan da suka hada da amfani da sakon banki na bogi wurin biyan kayan da suka siya tare da biyan karuwan da suka yi lalata da su.

Kakakin rundunar 'yan sandan, DSP Frank Mba, ya ja hankalin mutane da su gane cewa ana amfani da sakon banki na bogi wurin siyan kaya da damfarar mutane. Kamar yadda yace, an kama kashi na farko na masu laifin wadanda suka kware a tura sakon bogi na kudi daga banki ga wadanda suka damfara. Ya ce an kama su ne bayan sun biya wasu karuwai da wannan sakon bogin.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kano:Ganduje ya bada umarnin yi wa masu mukami a gwamnatinsa gwajin miyagun kwayoyi "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?