LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un: An tsinci gawar yarinya ‘yar shekara 6 da aka yiwa fyade a Masallaci a KadunaAn tsinci gawar wata yarinya ‘yar shekara shida da aka yiwa fyade a cikin Masallaci dake New Road, Kurmi Mashi kusa da babbar hanyar Nnamdi Azikwe, cikin jihar Kaduna.

Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa lamarin ya faru a ranar Juma’a, inda ya jawo hankalin mutane da yawa ciki hadda mambobin kungiyoyi zuwa wajen da lamarin ya faru.

Sai da aka sha fama da iyayen yarinyar kafin su bari a kai gawar yarinyar zuwa asibiti domin gabatar da bincik.

Da aka tuntube shi a waya, jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar ASP Muhammed Jalinge ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, “Duk da dai babu wanda aka kama har yanzu dake da hannu da wannan laifi, amma ‘yan sandan dake aiki a yankin na Kurmin Mashi tuni sun fara gabatar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

“Kwarai kuwa, an kawo karar lamarin a ofishin ‘yan sanda na Kurmin Mashi. Mutanen mu dake ofishin sun samu kiran waya akan cewa sun ga gawa kwance a cikin Masallaci.

“Sakamakon dokar hana zirga-zirga da aka sanya a jihar, ba a bude Masallacin sai ranar Juma’a kawai, sun iske gawar yarinyar da misalin karfe 3:20 na yamma gabanin sallar La’asar.

“Tuni an fara gabatar da bincike akan lamarin. Babu wanda aka kama dai har yanzu. Amma jami’an ‘yan sanda na ofishin Kurmin Mashi sun dauki lamarin da matukar muhimmanci. Saboda haka da mun kama wani zan sanar da ku.” Cewar Jalinge.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments