LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Hoton jana'izar dattijon da motocin Buratai suka kashe a KatsinaAn yi jana'izar dattijon da ya rasa ransa a wani hatsarin mota da ya danganci ayarin motocin wani Kwamandan sojin kasa na Najeriya, Birgediya Janar Warrah Idris. Hatsarin ya auku ne a ranar Litinin cikin jihar Katsina, yayin da ayarin motocin kwamandan sojin suka buge dattijon yana haye a kan baburinsa.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Alhaji Salisu Ibrahim, ya yi gamo da ajali ne bayan da ayarin motocin ke hanyarsu ta dawowa wajen daukan babban sojan bayan sun tsaya shan mai. Mashaida wannan mummunan lamari sun bayyana cewa hatsarin ya auku ne a daura a kwanar gidan Mani da ke kwaryar birnin Katsina. An tattaro cewa, dattijon mai shekaru 75 nan take ya mutu.

Mukaddashin kakakin rundunar sojin kasa na Najeriya, Kanal Sagir Musa, ya tabbatar da wannan lamari cikin wata sanarwa da ya fitar. Ya ce tawagar dakarun sojin wanda Birgediya Janar Idris ya jagoranta, ta ziyarci iyalan marigayi Salisu Ibrahim domin jajanta musu.

Sa dai a rahoton da jaridar Sahara Reporters ta ruwaito, ya bayyana cewa, ayarin motocin Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ne suka buge dattijon.

Haka kuma Jaridar Aminiya ta ce dattijon mai inkiyar 'Yar Yara ya rasa ransa ne a yayin da ya ke kan hanyarsa ta kai katin gayyatar daurin auren diyarsa da za a yi ranar Juma'a mai zuwa. Kamar yadda jaridar ta ruwaito, "wani ganau ya ce ya ga lokacin da ayarin motocin sojin da ke gudu suka buge tsohon a kan layin Yahaya Madaki da ke cikin birnin Katsina."

"Salisu Ibrahim ya rasa ransa ne sadda ya zo ketare hanya a kusa da Gidan Mani inda motocin suka dake shi kuma nan take ya riga mu gidan gaskiya." "Motar da ke cikin ayarin da ta bige dattijon dai ba ta tsaya ba ko kuma direban ya nuna nadamar abin da ya faru", inji shi.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments