--
George Floyd: Hanya uku da ake tauye wa baƙaƙen fata haƙƙi a Amurka

George Floyd: Hanya uku da ake tauye wa baƙaƙen fata haƙƙi a Amurka



ROHOTON: BBC HAUSA

Rikici ya barke a wasu birane a fadin Amurka kan kisan Ba'amurke bakar fata George Floyd, bayan da wani dan sanda ya makure masa wuya a Minneapolis.

Mun yi duba kan wasu bayanai na aikata manyan laifuka da shari'a a Amurka, da kuma abin da hakan ke nunawa game da abin da Amurkawa bakaken fata ke fuskanta idan aka zo batun doka da oda.

1. Amurkawa bakaken fata sun fi fuskantar hadarin mutuwa daga harbin bindiga

Alkaluman da ake da su na irin yanayin da 'yan sanda suka harbi tare da kashe mutane sun nuna cewa akwai yiwuwar Amurkawa bakaken fata su ci gaba da fuskantar barazanar kisa ta hanyar harbi idan aka duba yawansu a Amurka.

A takaice dai, a shekarar 2019, duk da cewa yawan Amurkawa bakaken fata ya kai kashi 14 cikin 100 na al'ummar kasar (duba da alkaluman kidaya na hukuma), su ne kashi 23 cikin 100 na yawan wadanda 'yan sanda suka kashe cikin mutum 1,000.

Kuma tun shekarar 2017 wannan adadi bai sauya ba, inda yawan fararen fata da ake kashewa kuma ke ta raguwa tun lokacin.

2. Ana yawan kama Amurkawa bakaken fata saboda shaye-shaye

An fi kama Amurkawa bakaken fata fiye da Amurkawa farare, duk da cewa bincike ya nuna babu bambanci tsakaninsu wurin yawan amfani da kayan maye.

A shekarar 2018, an kama kusan mutum 750 cikin duk mutum 100,000 na Amurkawa bakaken fata kan shan kayan maye, idan aka kwatanta da inda ake samun irin hakan cikin Amurkawa fararen fata da kusan mutum 350 cikin 100,000 ke irin wannan halayya ta shan kayan maye.

Wani tsohon binciken kasar kan amfani da kayan maye ya nuna yadda Amurkawa fararen fata ke amfani da kayan maye kai da kai da bakaken fata, amma sai aka fi ci gaba da kama bakaken fatar.

Misali, wani bincike da wata Kungiyar Neman 'Yanci Ta Amurka ta yi ya gano cewa Amurkawa bakaken fata sun fi fuskantar yiwuwar a kama su sau 3.7 kan amfani da wiwi fiye da fararen fata, duk da cewa yadda duka bangarorin ke amfani da wiwi din kai daya ne.

3. An fi ɗaure Amurkawa baƙaƙen fata

An fi ɗaure Amurkawa baƙaƙen fata sau biyar fiye da yadda ake ɗaure fararen fata, kuma fiye da sau biyu na yadda ake ɗaure Amurkawa 'yan asalin Sifaniya, a cewar bayanan baya-bayan nan.

A shekarar 2018, Amurkawa baƙaƙen fata ne suka mamaye kashi 13 cikin 100 na yawan al'ummar Amurka, amma su ne kashi uku cikin huɗu na yawan waɗanda ke tsare a gidajen yarin ƙasar.

Amurkawa fararen fata su ne kashi 30 cikin 100 na yawan waɗanda ke tsare a gidajen yarin ƙasar - duk da cewa su suke wakiltar kashi 60 cikin 100 na yawan al'ummar Amurkan.

Hakan na nufin akwai fiye da Amurkawa baƙaƙen fata 1,000 da ke gidajen yari cikin duk Amurkawa baƙaƙen fata 100,000, idan aka kwatanta da fararen fata 200 cikin duk 100,000 da ke gidajen yari.

An bayyana yawan mutanen da ke tsare a gidajen yarin Amurka a matsayin kowanne su zai yi zaman fiye da shekara daya a gidan yarin jiha ko na tarayya

Yawan Amurkawa baƙaƙen fata da ake ɗaurewa a gidan yari ya ragu cikin shekara 10 da suka gabata, amma har yanzu su ne suka fi yawa a gidajen yari fiye da kowace ƙabila.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com





KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "George Floyd: Hanya uku da ake tauye wa baƙaƙen fata haƙƙi a Amurka"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?