--
Gasar Firimiya: Mufti Menk ya ce akwai darasi a nasarar Liverpool

Gasar Firimiya: Mufti Menk ya ce akwai darasi a nasarar Liverpool



A jiya Alhamis, 26 ga watan Yuni, 2020, Jurgen Klopp ya kafa tarihin zama kocin farko da ya kai kungiyar Liverpool ga samun nasara a gasar 'Firimiya' na kasar Ingila. Liverpool ta shafe shekara da shekaru ba ta samu damar cin gasar kwallon kafa na Ingila ba, tun da aka canza masa salo da suna a cikin watan Fubrairun shekarar 1992.

Mufti Menk wanda shararren malamin addinin musulunci ne a Duniya, ya yi magana game da wannan nasara da Liverpool ta samu bayan ta sha jira na tsawon lokaci. A cewar Malamin, akwai abin koyi a cikin gwagarmayar da Liverpool ta yi na shekaru 30 kafin Chelsea ta yi wa kungiyar alfarmar doke Man City a Stamford Bridge jiya. A shafinsa na sada sada zumunta na Twitter, Shehin ya rubuta:

“Ka da ka taba karaya! Ka da ka taba! Bayan shekaru 30! Kungiyar Liverpool (ta lashe gasar) Firimiya. Never give up! Never! #30YearsLater #Liverpool #PremierLeague - Mufti Menk.

Wannan magana ta Mufti Menk ta jawo masa martani daga fiye da mutum 1, 200, Sannan mutane kusan 17, 000 su ka nanata sakon duk daga daren yau zuwa yanzu. Mutane fiye da 40, 000 ne su ka nuna cewa wannan sako na malamin addinin ya ba su sha’awa. Wasu sun yi ta sukar malamin, inda su ke ganin cewa ya saki layin koyar da addini, ya shiga harkar kwallon, abin da ake yi wa kallon gafala ko ma haramun.

Wani mutumi mai suna Jabir a shafin Twitter, ya nemi Malamin ya rabu da sha’anin Duniya, ya maida hankali kan addini. Wannan ya jawo shehin ya maida martani. Da ya ke wanke kansa daga zargi Mufti Menk ya rubuta: “Kwantar da hankalinka!

 Idan aka karbi addu’ar mutum bayan shekaru 30 ana roko, farin cikin ya isa ya kauda duk wani bakin ciki na baya, tabbas akwai darasi a gabanmu.” Ya kara da cewa: “Ka da a karaya! Kuma ban taba daukar bangare ba. Sako ne na addini. Idan zan kara, sai in ce lokacin ka ne da za ka yi addu’a.”

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Gasar Firimiya: Mufti Menk ya ce akwai darasi a nasarar Liverpool "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?