LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Barkwanci kawai ka keyi, ba zamu koma aiki ba - Likitoci sun yiwa minista raddiROHOTON: LEGIT.NG

Kungiyar Likitocin Najeriya ta siffanta barazanar gwamnatin tarayya na sallamarsu daga aiki ko kin biyansu albashi idan basu koma bakin aiki ba a matsayin wasan yara.

Shugaban kungiyar, Aliyu Sokomba, ya bayyana cewa "barkwanci kawai gwamnati keyi" kuma ko kadan hakan ba zai baiwa Likitoci tsoro ba.

Hakazalika ya lashi takobin cewa za su cigaba da yajin aikinsu har sai an biyasu dukkan bukatunsu.

A ranar Talata, gwamnatin tarayya ta yi barazanar sallamar likitocinta daga aiki muddin ba su yi watsi da maganar zuwa yajin-aiki, su ka koma asibitoci domin su cigaba da kula da marasa lafiya ba.

Gwamnatin Najeriya ta umurci likitocin su koma aiki a ranar Laraba, inda ta ce za ayi bincike kuma a hukunta duk wanda aka samu bai hallara a asibiti ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnati ta bukaci shugabannin asibitoci su rika ajiye littafin da za a rika sa hannu a duk lokacin da aka shiga ofis domin a tabbatar da masu zuwa aiki.

Wannan barazana ta fito ne daga bakin ministan harkar lafiya na kasa, Osagie Ehanire, bayan an gaza samun matsaya a zaman tattaunawar da su ka yi da kungiyar manyan likitocin.

Kungiyar NARD likitoci mataki na biyu a Najeriya sun shiga yajin aiki ne a ranar Litinin. Har yanzu dai ministan harkar kiwon lafiyan ya gaza shawo kan likitocin kasar.

A zaman da aka yi ranar Talata wanda aka fara da kimanin karfe 1:00, an tashi baram-baram babu matsaya tsakanin bangarorin inda shugaban NARD, Aliyu Socumba, ya fice a fusace.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments