--
Ba zamu kara saka dokar kulle ba - Gwamnatin tarayya

Ba zamu kara saka dokar kulle ba - Gwamnatin tarayya



ROHOTON: LEGIT.NG

Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da yasa ba lallai ta kara saka dokar kulle a kasa saboda hauhawar masu kamuwa da annobar korona ba. Shugaban kwamitin kar ta kwana a kan annobar korona (PTF), sannan sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis yayin taron hadin gwuiwa da kwamitin PTF ya saba gudanarwa. "Kamar yadda na fada a baya, zamu sake duba na tsanaki a kan yanayin da ake ciki.

Duk matakin da zamu dauka a nan gaba zai kasance bisa shawarar masana da kwararru a bangaren kimiyya da kuma sauran masu ruwa da tsaki. "Sannan dole mu duba halin da gwamnatinmu ke ciki, mu duba irin nasarorin da muke son cimma da kuma sake duban abubuwan da suka faru a tsawon sati biyar da aka yi a cikin dokar kulle," a cewar Boss Mustapha.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Malaman addini a karkashin inuwar United Muslim Foundation (UMS), a ranar Alhamis sun yi taro a Zaria don sake duba sharuddan dage dokar kulle a jihar Kaduna. A yayin zantawa da manema labarai bayan taron da aka yi a cibiyar matasa da ke Tudun Wada, Zaria, Malam Tukur Isa,

shugaban JIBWIS na jihar, ya ce sun amince da sharuddan. Ya kara da cewa: "Amma kuma muna son yin amfani da wannan damar wurin sanar da gwamna cewa malaman addini ne ke da hakkin sanar da matsayarsu a fannin addini yayin annoba. "A don haka, rashin mutuntawa ne a dinga bai wa malaman addini umarni wadanda suke wakiltar.

"A wannan lokacin na kulle, gwamnan yana kiranmu ne kawai ya bamu umarni kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana. Ba a taba tuntubarmu ba sai dai a bamu umarni. Malaman addini karkashin inuwar United Muslim Foundation (UMS), a ranar Alhamis sun yi taro a Zaria don sake duba sharuddan dage dokar kulle a jihar Kaduna. A yayin zantawa da manema labarai bayan taron da aka yi a cibiyar matasa da ke Tudun Wada, Zaria,

Malam Tukur Isa, shugaban JIBWIS na jihar, ya ce sun amince da sharuddan. Ya kara da cewa: "Amma kuma muna son yin amfani da wannan damar wurin sanar da gwamna cewa malaman addini ne ke da hakkin sanar da matsayarsu a fannin addini yayin annoba. "A don haka, rashin mutuntawa ne a dinga bai wa malaman addini umarni wadanda suke wakiltar.

"A wannan lokacin na kulle, gwamnan yana kiranmu ne kawai ya bamu umarni kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana. Ba a taba tuntubarmu ba sai dai a bamu umarni.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Ba zamu kara saka dokar kulle ba - Gwamnatin tarayya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?