--
Ba zamu bude Masallatai da coci-coci ba - Gwamnatin Legas

Ba zamu bude Masallatai da coci-coci ba - Gwamnatin Legas



ROHOTON: LEGIT.NG

Bayan tattaunawa da rashin cimma matsaya kan lamarin bude wuraren ibada tsakanin gwamnatin jihar da shugabannin addini, gwamnatin jihar Legas ta ce Masallatai da coci-coci su cigaba da kasancewa a garkame.


Kwamishanan harkokin gida na Legas, Annofiu Elegushi, ya bayyana hakan ne yayinda yake hira da manema labarai a taron murnan cikar gwamnan Legas shekara 1 kan karagar mulki. Ya ce babu yiwuwan bude Masallatai da Coci-coci a yanzu. A cewarsa,


"tun kafin gwamnatin tarayya ta yi sanarwa, muna ganawa da shugabannin addini, kuma mun zauna da hukumar kare al'umma, kan yiwuwan bude wuraren ibada."


" Ina mai fada muku da tabbaci cewa a ganawar, an yi ittifaki ba za'a bude wuraren ibada ba." "Sunce ba za su iya hana mutane sama da 20 Sallah a bayasu ba, kamar yadda wani limamin ya fadi, ba zai san abinda ke faruwa a bayansa ba idan ya tayar da Sallah."


"Saboda haka an kawar da maganan bude wuraren ibada har sai lokacin da aka tabbatar abubuwa sun daidaita." "Gwamnatin tarayya ta sanar da haka, amma bata ce jihohi basu da ta cewa ba, saboda haka dukkan jihohi su duba lamarin jihohinsu."

A jiya Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da shawarar kwamitin kar ta kwanan fadar shugaban kasa kan cutar COVID-19 PTF na sassauta dokokin da aka kafa domin takaita yaduwar cutar.


Shugaban kwamitin wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da hakan a hira da manema labarai ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2020.


Yace: "PTF ta mika shawarinta kuma shugaba Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a aiwatar da su cikin makonni hudu masu zuwa fari daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni, 2020."


"An sassauta dokar hana taruwa a wuraren Ibada bisa ga sharudan da PTF ta gindaya da kuma yardar gwamnatocin jihohi." "Za'a amince a rika shiga kasuwanni da wuraren tattalin arziki amma da lura saboda takaita yaduwar."


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice



LATSANAN DOMIN SAMUN LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "Ba zamu bude Masallatai da coci-coci ba - Gwamnatin Legas"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?