--
'An kashe sojoji 20 da farar hula 40 a Borno'

'An kashe sojoji 20 da farar hula 40 a Borno'

A kalla sojoji 20 da farar hula sama da 40 aka kashe a wasu tagwayen hare-hare da aka kai a jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Mazauna yankin sun shaida cewa 'yan bindiga masu ɗauke da muggan makamai ciki har da na harba roka suka shiga garin Monguno, wanda a nan matattarar ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasashen waje suke.

Hare-haren da aka kai a Monguno da Nganzai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan 'yan tayar da ƙayar baya sun kashe a kalla mutum 81 a wani hari da suka kai a ƙauyen Gubio. Kungiyar ISWAP wadda ke iƙirarin jihadi a ƙasashen yammacin Afirka ta fito fili ta ɗauki nauyin kai duka hare-haren uku. A garin Mongunu, wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana cewa mayaƙan sun ƙone matattarar hukumomin bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya tare da kuma ƙona wani ofishin 'yan sanda.

A garin Nganzai, mayaƙan sun shiga garin ne kan babura da kuma motoci ƙirar akori kura inda suka kashe mazauna ƙauyen fiye da 40.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗaruruwan farar hula ne aka raunata inda kuma asibitin garin ya cika maƙil har ake tilasta wa wasu masu raunuka da su tsaya a waje.

Mayaƙan sun rarraba takardu ga mazauna garin mai ɗauke da gargaɗi inda aka yi rubutun da Hausa, suka gargaɗe su da kada su yi aiki da sojoji ko kuma ƙungiyoyin bayar da agaji na ƙasashen waje.

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da kai wannan harin a wata sanarwa da ta fitar.

Sai dai a wani ɓangaren sojojin Najeriya sun mayar da martani kan wannan hari inda suka jinjina wa sojojin ƙasar bisa namijin ƙoƙarin da suka yi wurin daƙile harin da aka kai a Mungonu. Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce babban hafsan sojojin ƙasa na Najeriyar ya ji daɗi matuƙa kan yadda sojojin suka yi fatafata da mayaƙan da kuma ƙwato wasu makamansu.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "'An kashe sojoji 20 da farar hula 40 a Borno'"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?