LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

2023: Kar ku zabi duk dan takarar da aka tsayar a APC ko PDP - Matasan arewa ga 'yan NajeriyaShugaban kungiyar tuntubar matasan arewa, Shetima Yerima, ya ce shugaba Buhari ya gaza wajen sarrafa akalar mulkin Najeriya kamar yadda ya kamata. Yayin wata hirarsa da manema labarai a Kaduna, Yerima ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da 'yan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC ko PDP a shekarar 2023.

Kazalika, ya shawarci 'yan Najeriya su duba wani hazikin mutum mai kishi da za su zaba a matsayin shugaba a karkashin wata sabuwar jam'iyyar daban, banda APC ko PDP. A cewar Yerima, 'yan Najeriya, musamman mutanen arewa basu amfana da komai ba a gwamnatin shugaba Buhari,

a saboda haka babu wani sauran uzurin zaben jam'iyyar APC ko PDP a shekarar 2023. Ya kara da cewa kungiyarsa ta na aiki tukuru domin kafa wata tafiyar hadaka da za ta fito da dan sabon dan takarar shugaban kasa da zai kawowa Najeriya sauyin da manyan jam'iyyun da suka yi mulki suka gaza samarwa.

"Tun bayan da Buhari ya shafe watanni shidda kafin ya nada ministocinsa na farko na fahimci cewa akwai matsala. "Tun shekarar 2003 Buhari ya ke neman kujerar shugaban kasa, amma ya shafe watanni shidda tunanin mutanen da zai nada domin su taya shi aiki," a cewar Yerima

Yerima ya bayyana cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, basu cancanta a zabesu ba a 2023.

Da yake karin bayani a kan irin gwagwarmayar da ya sha fama da ita domin tabbatar da dorewar mulkin dimokradiyya, Yerima ya zargi wasu tsirarun mutane da kulla makirci kala - kala domin ganin sun cigaba da mulkar jama'a ta kowacce hanya.

Shugaban kungiyar matasan ya ce a yanzu haka bashi da wani gwani a cikin 'yan siyasar Najeriya. Kazalika, ya bayyana cewa shugaba Buhari ne ya kamata ya zama kwatankwacin Mandela a Najeriya amma shi ma yanzu ya bi sahun sauran shugabannin da za a cigaba da ambaton sunansu idan ana batun shugabannin da suka gaza fita kunyar talaka.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN
 LABARI TA WHATSAPP: https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments