--
12 ga watan Yuni: Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun ranar Juma'a

12 ga watan Yuni: Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun ranar Juma'a

ROHOTON: LEGIT.NG

Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta ayyana ranar Juma'a, 12 ga watan Yuni, a matsayin ranar hutun aiki domin gudanar da bikin ranar Dimokuradiyya ta wannan shekara. Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya ayyana ranar hutun a madadin gwamnatin tarayyar kasar. Ya na mai taya daukacin al'ummar Najeriya na nan gida da kuma wadanda suke ketare,

murnar zagayowar wannan rana da aka sauya salon mulki daga hannu soji ya koma hannun farar hula. Ministan ya jinjinawa gwarazan mutanen da suka taka rawar gani wajen sadaukarwar da ta tabbatar da komawa kan tsarin mulki na Dimokuradiya a kasar nan.

Sanarwar hakan ta fito ne daga ma'aikatar harkokin cikin gida wadda sakatariyar dindindin ta ma'aikatar, Georgina Ehuriah, ta rattaba wa hannu a madadin Ministan.

Cikin sanarwar, Aregbesola yana kira ga dukkan 'yan Najeriya da su ci gaba da mutunta kokarin sadaukar da kan da akayi wajen samun mulkin dimokuradiyya a Najeriya.
Ministan Harkokin Cikin Gida: Rauf Aregbesola Source: Depositphotos 

Ya nemi 'yan Najeriya da su bai wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari hadin kai domin tabbatar da manufofin da za su ci gaba malalo musu romon Dimokuradiya. Ya ce kuma kada a manta da gwagwarmayar da masu kishin kasa na baya suka yi har ta kai ga wasunsu sun sadaukar da rayukansu domin tabbatuwar tsarin shugabanci na Dimokuradiya.

Ministan ya kuma ba da tabbacin hobbasan da gwamnatin Tarayya ta ke yi wajen yakar annobar cutar korona, inda ya nemi hadin kan duk 'yan Najeriya da su dauki nauyin dakile yaduwar cutar. Ya jaddada bukatar dukkanin 'yan Najeriya su dabi'antu da kiyaye dokokin da muhukuntan lafiya suka gindaya musamman bayar da tazara da yin nesa-nesa da juna.

Haka kuma ya shawarci al'ummar kasar a kan yin kyakkyawan riko da ingantacciyar tsaftar jiki, mahalli da kuma ta zamantakewa domin tsare lafiyarsu. Shekarun baya, an saba gudanar da bikin ranar dimokuradiya a ranar 29 ga watan Mayu na kowace shekara gabanin shugaba Buhari ya sauya ranar a shekarar 2018. Buhari ya yi hakan ne domin karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar ta GCFR, domin tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Ana ganin marigayi Abiola ne ya lashe zaben wanda gwamnatin mulkin soja ta wancan lokacin ta soke shi, kuma galibin 'yan kasar na ganin shi ne zabe mafi sahihanci a tarihin siyasar kasar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/






KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "12 ga watan Yuni: Gwamnatin Tarayya ta ba da hutun ranar Juma'a "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?