LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Zamu rusa duk gwamnatin da tayi yaki da Almajiranci - Almajirai sunyi gargadiAlmajirai a fadin tarayya sun yi gargadi da babban murya ga gwamnatin tarayya da na jihohi kan yadda ake yawo da Almajirai daga jiha zuwa jiha da sunan mayar da su jihohinsu na asali, Rahoton New Telegraph. Yayin bayyana bacin ransu, shugaban cibiyar karatun Al-Qur'ani na tarayya, Sheikh Hassan Musa,

a ranar Juma'a yace "ya kamata gwamnatoci su yi hattara kan lamarin Almajirai saboda duk gwamnatin da tayi yaki da Almajiranci za ta rushe ko shakka babu." Sheikh Musa, wanda ya bayyana hakan a taron kaddamar da cibiyar killace Almajirai dake Tudun Fulani Hajj Camp, dake Minna,

babbar birnin jihar Neja, ya ce kada a manta abinda suka yiwa gwamnatin Jonathan. Ya ce kada a manta yadda Almajiran Najeriya suka kawar da gwamnatin Goodluck Jonathan a shekarar 2015 saboda maganar da uwargidarsa, Patience Jonathan, tayi kan Almajirai.

Yace: "Adadin almajirai a Najeriya ya zarce milyan 16 kuma mun goyi bayan gwamnatin All Progressives Congress (APC) a 2015 saboda zagin da matar Jonathan, Dame Patience, tayi mana." "Yadda tayi magana kanmu lokacin yakin neman zaben mijinta karo na biyu ya bata mana rai kuma wannan shine dalilin da yasa muka zabi shugaba Muhammadu Buhari."

"Mun yanke cewa Jonathan ba zai koma ba, saboda haka muka umurci dukkan almajiran Najeriya su zabi Buhari. Amma yanzu da ya lashe zabe, ga abin ake mana." Ya gargadi yan siyasar Najeriya kan wasa da lamarin Almajirai cewa "Za mu hadu da su a 2023."

A nasa jawabin, sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmad Matani, ya ce an samar da cibiyar killace Almajirai ne bisa shawaran da gwamnonin Arewa 19 suka yanke na mayar da Almajirai jihohinsu na asali.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments