--
Yaya ya fille hannun kaninsa sakamakon rikici daya kaure tsakaninsu a kan budurwa

Yaya ya fille hannun kaninsa sakamakon rikici daya kaure tsakaninsu a kan budurwa



Rikici ya balle tsakanin wasu yan biyu, watau Peter da Paul a jahar Imo a kan wata budurwa, wanda yasa Peter ya Sassari Paul da adda, daga bisani ala tilas aka datse masa hannu. Jaridar The Nation ta ruwaito rikicin ya faru ne a ranar Litinin, 25 ga watan Mayun a kauyen Ndimoko Arondizuogu na jahar Imo, inda Peter Ogbonna ya sassare dan uwansa Paul Ogbonna.

Majiyar ta bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan Paul ya sa tsumagiya ya bullae dan budurwar Peter a laokacin da ya je gidansu yana neman mahaifiyarsa. 

Dama Paul baya goyon bayan soyayyar Peter da wannan bazawara wanda ta haifi yara dai dai har guda biyar, amma koda Peter ya samu labarin dukan yaron da Paul ya yi sai ya harzuka. cikin fushi Peter ya rarumi wata adda mai kaifin tsiya, ya nufi gidansu inda ya tunkari tagwayen nasa, daga nan aka fara cacar baki, wanda ya juye zuwa fada, a nan ne Peter ya sassari Paul. 



Jama’an dake wurin da basu tsaya wata wata ba suka garzaya da Paul cibiyar kiwon lafiya ta gwamnatin tarayya dake garin Owerri jahar, inda dole aka datse masa hannuwa don ya rayu. Ba tare da bata lokaci ba jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Imo suka yi ram da mai laifin, wanda a yanzu haka yana daure a ofishin Yansanda dke Eke Ndizuogu. 

A wani labarin kuma, Akalla mutane 12 wanda yawancin su mata ne aka kashe a garin Oku na karamar hukumar Boki ta jahar Cross Rivers sakamakon zarginsu da ake yi maita da tsafe tsafe. Guardian ta ruwaito mutanen garin sun lakada ma matan dan banzan duka ne, 

daga bisani kuma suka cinna musu wuta wanda yayi sanadiyyar mutuwar yawanci daga cikinsu. Sai dai wata majiya da bata bayyana kanta ba ta bayyana cwa wani babban jami’in gwamnatin jahar Cross Rivers ne ya dauki nauyin kashe mutanen.



KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com




KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yaya ya fille hannun kaninsa sakamakon rikici daya kaure tsakaninsu a kan budurwa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?