--
'Yan bindiga 'sun kashe kusan mutum 60 a Sokoto'

'Yan bindiga 'sun kashe kusan mutum 60 a Sokoto'



ROHOTON: BBCHAUSA

Rahotanni daga jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya na cewa an kashe mutane kusan mutum 60 a cikin hare-haren da 'yan bindiga suka kai ranar Laraba a wasu kauyuka na karamar hukumar Sabon-Birnin-Gobir.

Ganau sun ce maharan sun kwashe sa'o'i suna ta'adi a kauyukan ba tare da kowa ya tunkare su ba.

Kazalika ganau sun ce wata mata da 'yan bindiga uku sun mutu a cikin wani harin da suka kai a karamar hukumar Gwadabawa.

Wani jami'i da ya je wuraren da lamarin ya faru ya shaida wa BBC cewa, da misalin karfe uku zuwa hudu har zuwa biyar na yammacin ranar Laraba, suka samu labarin cewa ga mutane nan sun taso da babura kusan 100 daga dajin da ke kusa da Issa sun nufi kauyukan.

Ya ce: "Ko da muka samu labari sai muka je muka sanar da jami'an tsaro ga abin da ke faruwa, haka har wadannan mutane suka isa garin Garki, anan suka fara daga garin Dan adu'a."

Jami'in ya ce "A wannan gari na Dan adu'a munga gawa a kwance har mutum 13, ban da wadanda ake nema, a garin Garki kuwa abin da idanuna suka nuna mini har na dauki hoto naga gawa 19".

A cewarsa: "A garin Kuzari, an kashe mutum 20 har da limamin garin, garin Kafi ma an kashe mutum 6, sai garin Masawa aka harbi mutum 2".

Ganau din ya ce idan aka hada jumillar mutanen da ya ga gawarsu sun kusa mutum 60, banda wadanda ake nema.

Ya kara da cewa: "Barayin shanu da mutane ne suka kai wadannan hari, wanda bai jima ba mai girma gwamna jiha ya kai jaje Sabon Birni a makon da ya wuce wato ranar jajiberin sallah domin jajantawa mutanen garin bisa kashe mutum 19 da aka yi".

"Batun jami'an tsaro mun shaida wa 'yan sanda na Sabon Birni ga abin da ke faruwa, nan kuma suka je garin Garki, to amma abin da ke faruwa basu da kayan aikin da zasu fafata da wadannan 'yan bindiga.

"Baya ga rashin isassun kayan aiki, sannan su kansu jami'an tsaron basu da yawan da zasu tunkari wadannan 'yan bindiga," in ji shi.

Jihar ta Sokoto na makwabtaka da jihar Zamfara wacce 'yan fashi da barayin shanu suka addaba.

A makon jiya ne kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "'Yan bindiga 'sun kashe kusan mutum 60 a Sokoto'"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?