--
Sarkin Musulmin Najeriya ya ce a saka takunkumi, a zauna a gida

Sarkin Musulmin Najeriya ya ce a saka takunkumi, a zauna a gida



Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bi sahu wurin wayar da kan al'umma kan yadda za su kare kansu daga kamuwa da cutar korona.

Wani sako da hukumar National Orientation Agency - hukuma mai wayar da kai ta Najeriya - ta wallafa a Twitter ya nuna hoton sarkin yana bayyana cewa cutar korona gaskiya ce.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira ga 'yan Najeriya da su sanya takunkumi kuma su zauna a gida domin kare lafiyarsu.

"An san sarakunan gargajiya da kasancewa kusa da al'umma a yankunansu, hakan kan sa su yi tasiri kan talakawansu," a cewar sakon.



  KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


  1. KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Sarkin Musulmin Najeriya ya ce a saka takunkumi, a zauna a gida"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?