LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Matar aure ta zazzabga wa miji mari bayan ta kama shi da karuwa a otal (Bidiyo)

Wani bidiyon fusatacciyar mata da ta kama mijinta da wata ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani - A bidiyon, matar aure ce ta dinga zabga wa mijinta mari bayan kama shi da tayi da budurwa a wurin cin abinci

Bata tsaya nan ba, ta watsa masa miyar abincin da ya siya tare da tabbatar masa da cewa za su hadu a gida A wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an ga wata mata ta fada mijinta da duka bayan ta kama shi da wata a wurin cin abinci. Bidiyon ya jawo cece-kuce daga jama'a wadanda suka ganshi.

Fusatacciyar matar ta kasa jure ganin mijinta da wata mata. Hakan ne yasa ta zazzabga masa mari masu matukar kara a fuskarta. Ta tambayeshi ta yadda ya samu kwarin guiwar da har ya fara mu'amala da wata mace bayan tana nan da ranta.

Bata tsaya a nan ba, ta watsa wa mijin miyar abincin da ya siya a gidan cin abincin tare da tabbatar mishi da cewa za su hadu a gida. A nan take ta juya tare da ficewa daga gidan cin abincin. Masu kallo sun sha matukar mamaki tare da tambayar magidancin yadda ya auri masifaffiyar mata haka. Sun ci gaba da yi mata tofin Alla-wadai game da wannan mummunar dabia'a da ta bayyana.

 A wani labari na daban, bayan rufe Masallatai na sama da watanni biyu, ma'aikatar al'amuran addinin Musulunci ta yi kira ga ma'aikatanta da su fara gyara da tsaftace manya da kananan Masallatai sama da 90,000 a masarautar. Za a bude Masallatan ne a ranar Lahadi mai zuwa amma banda Masallatan garin Makkah a wannan budewar.

Kamar yadda rahoton Saudi Gazette ya bayyana, za a bude Masallatan ne kamar yadda umarnin Ministan al'amuran addinin Musulunci, Dr. Abdullatif Al-Sheikh da kuma shawarwarin majalisar manyan malamai ta bayyana. Ma'aikatar na yakin wayar da kai a kafafen yada labarai, Talabijin, rediyo, jaridu da sauran kafafen yada labarai. Ana wannan wayar da kan ne don kiyaye hanyoyin yaduwar cutar ko bayan budewar Masallatai.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments