LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kasuwar musayar saye da siyar da 'yan kwallon kafaLeicester ta yi tayin bayar da kwangilar lokaci mai tsawo ga dan wasan Liverpool Adam Lallana. Kwangilar dan wasan mai shekara 32 dan kasar Ingila za ta kare a Anfield a karshen watan Yuni.(Football Insider)

Kungiyoyin Gasar Premier biyar -Chelsea, Newcastle, Manchester United, Arsenal da kuma Leicester- suna son dauko dan wasan Barcelona da Brazil Philippe Coutinho. Za a sayar da dan wasan mai shekara 27, wanda yake zaman aro a Bayern Munich, a kan £90m.(Mundo Deportivo - in Spanish)

Babu wata kungiya da ta yi tayin daukar dan wasan Real Madrid da Wales Gareth Bale don haka dan kwallon mai shekara 30 zai ci gaba da zama a kungiyar zuwa karin shekara daya.(Marca)

Manchester United da Newcastle suna son dauko dan wasan Uruguay Facundo Pellistri. A halin da ake ciki dan wasan dan shekara 18 yana buga tamaula a Penarol.(Mail)

Ku karanta wasu labarai anan:https://www.bzglobalservice.com.ng/


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments