--
Manyan kabilu 10 da suka fi shahara a nahiyar Afrika

Manyan kabilu 10 da suka fi shahara a nahiyar Afrika



ROHOTON: LEGIT.NG

Ubangiji ya albarkaci nahiyar Afrika da mutane hazaikai da kuma kabilu masu tarin yawa. Legit.ng ta tattara muku kabilu daban-daban da suka fi jama’a masu tarin yawa a nahiyar Afrika. Ga jerin kabilu 10 a nahiyar Afrika da suka fi kowacce kabila yawa kamar yadda Facts one ta bayyana.

1. Kabilar Hausa - miliyan 78: Tana da mutane a kalla miliyan 78 a fadin nahiyar Afrika. Ana samu masu yin yaren a kasashe masu tarin yawa na fadin haiyar.

 2. Igbo - miliyan 45: Da mutum miliyan 45 ne kabilar Ibo ta zama ta biyu a cikin kabilu mafi yawan mutane a nahiyar Afrika.

3. Yoruba - miliyan 44: Kabilar nan ce ke biye da kabilar Ibo a yawan mutane a nahiyar Afrika. Tana da mutane masu yawan miliyan 44.

4. Oromo - miliyan 40: Kabilar Oromo ce kabila ta hudu a yawan jama’a a nahiyar Afrika. Tana da mutum miliyan 40.

5. Fulani - miliyan 35: Kabilar Fulani ce ta biyar a wannan jerin, tana da mutane miliyan 35 a nahiyar Afrika.

6. Amhara - miliyan 20.2: Kabilar ce ta shida a wannan jerin kuma tana da jama’a miliyan 20.2

7. Akan - miliyan 20: Akan kabila ce da ke da yawan mutane har miliyan 20 a fadin nahiyar Afrika.

8. Somali - miliyan 20: Kabilar Somali c eke biye da Akan wacce ke da miliyan 20 na jama’a.

9. Hutu - miliyan 18.5: Kabilar tana da jama’a miliyan 18.5 na masu yin yarenta a Afrika.

10. Ijaw - miliyan 15: Kabilar Ijaw ce ta karshe kuma ta goma a wannan jerin. Tana da mutane miliyan 15 da ke yin yaren a Afrika.


A baya mun kawo cewa, yaren Hausa ne yaren da aka fi yi kuma mafi dadewa a cikin yankin mutane miliyan 120 kamar yadda aka gano. Masu yin yaren na nan dankam a kasashen Najeriya, Nijar, Chadi, jamhuriyar Benin, Kamaru, Togo, jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Ghana, Sudan, Eritrea, Guinea, Gabon, Senegal da Gambia.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Manyan kabilu 10 da suka fi shahara a nahiyar Afrika"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?