--
Katsina: Sama da mutum 600 suka samu mafaka a filin kwallo bayan harin 'yan bindiga (Hotuna)

Katsina: Sama da mutum 600 suka samu mafaka a filin kwallo bayan harin 'yan bindiga (Hotuna)

ROHOTON: LEGIT.NG

A kalla mutum 600, wadanda suka hada da mata da kananan yara 'yan bindiga suka fatattaka a fadin jihar Katsina sannan suka samu masauki a filin kwallo da ke ATC a Katsina. 'Yan gudun hijira masu tarin yawa na ci gaba da tururuwa zuwa filin kwallon inda suke kira ga jama'a don kai musu tallafin abinci.

'Yan gudun hijirar na ci gaba da tururuwar samun mafaka a cikin wasu sassa na jihar Katsina. A kalla mutane 400 ne suka samu masauki a garejin kanikawa na Bebeji inda mutum 360 suka samu mafaka a Yammawa. Hakazalika, sama da mutum 100 ne suka samu mafaka a Tudun Baras. Tsanantar hare-haren 'yan bindiga da ya addabi jama'ar kananan hukumomin Batsari, Safana, Jibia, Kankara, Dandume, Faskari da Sabuwa ya hana mazauna yakin da dama zaman gidajensu.


Idan za mu tuna, gwamnatin jihar Katsina ta shiga tattaunawa da 'yan bindigar da suka addabi yankin, tare da alkawarin rangwame garesu. Yara kanana da mata sune aka fi gani a cikin kwanakin nan suna kaiwa da kawowa tare da bara a fadin jihar don samun abinci.

A wani labari na daban, rundunar sojin hadin guiwa (MNJTF) ta ragargaji mayakan ta'addancin ISWAP a yankunan tsibirin tafkin Chadi, kamar yadda majiya daga rundunar ta sanar. "Bayan samun bayanan sirri daga majiyoyi daban-daban, mun samu bayanai inda 'yan ta'addan suka rike a Tumbun tare da gano sansani, wurin adana makamai da sauran abubuwan amfanin 'yan ta'addan. "Dogaro da hakan,

 dakarun sun kai samame ta jiragen yaki, an ragargaza ababen amfanin 'yan ta'addan," majiyar tace. Sakamakon samamen ya bayyana cewa an halaka 'yan ta'addan masu tarin yawa tare da kona gine-ginen 'yan ta'addan. Tashin bama-bamai daga bidiyon ya bayyana cewa an kone ababen hawa da ma'adanar man fetur din 'yan ta'addan. Hakazalika, jiragen yakin kasar Chadi sun kai samame a Tumbun, shugaban fannin yada labarai na dakarun kasar Chadi, Kanal Timothy Antigha, yace a wata takarda.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Katsina: Sama da mutum 600 suka samu mafaka a filin kwallo bayan harin 'yan bindiga (Hotuna)"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?