--
Karfin hali: Yadda kwarto ya bi mijin mata har gida ya datse masa hannu

Karfin hali: Yadda kwarto ya bi mijin mata har gida ya datse masa hannu

ROHOTON: LEGIT.NG

'Yan sanda sun kama wani mutum, Kamoru Ajibola a unguwar Amuda Oba da ke Modakeke a jihar Osun a kan cewa ya datse hannun wani mutum bayan zarginsa da kwartanci.



An kuma kama abokin Ajibola mai suna Ismailha Mohammed da aka ce shima ya taimaka wurin datse hannun hagu na Tunji Ajayi. The Nation ta ruwaito cewa Ajibola da Mohammed sun kai wa Ajayi hari ne a ranar Litinin bayan ya zargi Ajibola na zina da matarsa Kemi.



Wani mazaunin unguwar ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa alakar kwartanci da ke tsakanin Kemi da Ajibola ba sabon abu bane. "Hakan ya yi sanadin rikici tsakanin mutanen biyu amma a safiyar yau, Ajibola da abokinsa suka zo nan suka yi wa mijin Kemi rauni."



Mai magana da yawun rundunar yan sanda a jihar, Yemisi Opalola ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce wadanda ake zargin suna hannu kuma ana cigaba da bincike. A wani labarin, mun kawo muku cewa wani bawan Allah da ba a bayyana sunansa ba ya yanke jiki ya mutu a yayin da ake bikin sallar Idi a unguwar Sharada a jihar Kano.



Vangaurd ta ruwaito cewa mutumin ya yanke jiki ya fadi kuma ya mutu ba da dadewa ba bayan ya gama sallar raka'a biyu na Idi a Kano. Wata majiya da ta tabbatar da afkuwar lamarin amma ba ta fadi sunan mutumin ba ta ce mutumin ya fito daga unguwar Kofar Dan Agundi ne domin ya yi sallar Idi a Sharada. Acewarsa, "Ba mu san sunanshi ba,



ko adireshinsa ko inda ya ke aiki da sauran bayanai. "Mun dai san daga Kofar Dan Agundi ya taho domin yin salla a Sharada. Ya yanke jiki ya fadi bayan an kammala sallar." "Yan uwansa da jamian hukumar Hisbah sun dauke gawarsa. Sun koma da shi Kofar Dan Agundi inda aka yi masa jana'iza bisa tsarin koyarwar addinin musulunci," a cewar majiyar.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Karfin hali: Yadda kwarto ya bi mijin mata har gida ya datse masa hannu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?