--
Kashe-kashe a arewa: Jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati - Gwamnan APC

Kashe-kashe a arewa: Jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati - Gwamnan APC



ROHOTON: https://hausa.legit.ng/news/

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya ce barazanar rashin tsaro da ke addabar arewa maso yamma ta sa jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati - Kamar yadda gwamnan ya bayyana yayin zantawa da shugaban sashen horarwa na tsaro, Janar Leo Irabor, ya ce mazauna jiharsa sun fara tunkarar 'yan bindigar

- Aminu Masari ya ce annobar korona ce ke rufe yawan kashe-kashen da ake samu a yankin arewa maso yammacin kasar nan Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari a jiya Laraba ya ce barazanar rashin tsaro da ke addabar yankin Arewa maso yamma da jihar Katsina ya sa jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati. A yayin zantawa da shugaban horarwa, Janar Leo Irabor wanda ya kai masa ziyara,

ya ce mazauna jihar sun fara kokarin tunkarar 'yan bindigar don hare-haren kullum kara yawaita suke. "A halin yanzu ina cikin rudani. Ina da kayyadaddun kayan aiki da jami'ai. A tunanina idan aka karfafa jihar nan da kayan aiki da ma'aikata, za mu ga karshen wannan jarabawar," yace.

"Halin da yankin Arewa maso yamma ke ciki abin tashin hankali ne. Annobar Coronavirus ce ke rufe labaran kashe-kashen da 'yan bindiga ke yi a yankunan. A koda yaushe muna cikin barazana ne," yace. Masari ya kara da cewa, "A bangarena, zan iya cewa 'yan bindigar nan sun fi dabbobi hatsari saboda basu da ilimi kowanne iri. Suna al'amuransu ne tamkar ba musulmai ba.

"Sulhun da muka yi dasu yana amfani a wurare amma baya amfani a wasu. Muna bukatar zaman lafiya ya dawo yankunan mu. Sai kuwa an kawar da 'yan bindiga ne kadai za mu samu hakan." Tun farko, Janar Irabor ya ce sun isa jihar ne don ganin gaskiyar yadda al'amura suke sannan su kokarta wurin kawo gyara, jaridar Daily Trust ta ruwaito. Sanannen abu ne cewa 'yan bindiga sun gallabi yankin arewa maso yamma na kasar nan yayin da Boko Haram suka yi katutu a yankin arewa maso gabas.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Kashe-kashe a arewa: Jama'a sun dawo daga rakiyar gwamnati - Gwamnan APC"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?