--
Coronavirus: An tilasta wa wasu limamai share gidan hakimi a Kano

Coronavirus: An tilasta wa wasu limamai share gidan hakimi a Kano



ROHOTON: https://www.bbc.com/hausa

An kama wasu limamai da suka karya dokar hana taron jama'a suka ja mutane sallar Juma'a a karamar hukumar Minjibir da ke Jihar Kano, inda aka yi musu hukunci share kofar gidan hakimi har tsawon mako guda.


Kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim ne ya bayyana wa BBC hakan a wata hira ranar Laraba.

Jibo Ibrahim ya kara da cewa baya ga hukuncin tilasta wa limaman yin shara an kuma ci tararsu naira 10,000 ko wanne,

A karshen makon da ya gabata ne dai aka kama wadannan limaman bayan sun ja dandazon mutane sallar juma'an a masallacin idi na wajen garin Minjibir, al'amarin da ya ja jami'an tsaro suka yi musu dirar mikiya.

Dangane kuma sauran shari'o'i masu alaka da annobar korona, Jibo Ibrahim ya ce kotunan tafi da gidanka 11 da aka kirkira a jihar domin tabbatar da dokar zaman gida, ya zuwa yanzu sun hukunta kararraki 717 daga ranar Lahadi 3 ga watan Mayu zuwa ranar Laraba 6 ga watan.

Daga cikin wadanda aka hukunta din akwai wadanda aka zane da bulala saboda karya kodar hana fitan da aka sa, a wani mataki na hana yaduwar cutar korona.

An dai ci tarar mutane da dama haka kuma an tilasta wa mutane da wasu da yawa ayyukan yau da kullum, kamar share-share

Akwai wadanda gwamna da kansa ya kama a kwanar Dan Gora, wadanda suka hada da manyan motoci kirar Hummer.

Cikin motocin da gwamnan jihar ya kama akwai wasu manyan motoci da suka dakko mutane za su shiga kano wanda bidiyonsu ya yi ta yawo a kafafen sadarwa, suma an ci tarar ko wacce naira 150,000.

Kazalika akwai wata mata da ake zargin ta samu rashin jituwa da ma'aikatan tsaro, bayan fitowa da ta yi daga gida ba tare da wata cikakkiyar shaida ba, an ci tararta kuma an tisa keyarta zuwa gidan tarbiya.

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da cutar korona ta yi kamari a Najeriya, kuma tsoron hakan ne ya sanya gwamnatin tarayya ta sanya dokar kulle ta mako biyu a jihar.


Kawo yanzu dai akwai mutum 427 da ke dauke da cutar korona a Kano.


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com



KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP


0 Response to "Coronavirus: An tilasta wa wasu limamai share gidan hakimi a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?