--
Coronavirus: Mene ne illolin sassauta dokar kulle a Kano ?

Coronavirus: Mene ne illolin sassauta dokar kulle a Kano ?

Masana harkokin lafiya da mutane daidaiku sun soma bayyana ra'ayoyinsu kan matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka kwatsam na sassauta dokar kulle duk da samun karuwa a yaduwar cutar korona a jihar.

Ranar Asabar, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ta Kano, ya sanar da sassauta dokar hana fitar wacce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya saka ta tsawon kwana 14.

Gwamnatin Kano ta ce mazauna birnin Kano za su iya fita a ranakun Litinin da Alhamis daga karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma domin sayen abinci da magani.

Sai dai gwamnan ya ce manyan kantunan sayayya ne kadai za su bude, yayin da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Gwamnan ya dauki matakin sassauta dokar kullen ne a daidai lokacin da cutar koron ke ta'azzara a jihar ta Kano.

A ranar Talatar makon da ya wuce ne Shugaba Muhammadu Buhari ya saka dokar hana fitar a jihar Kano sakamakon karin yawan mutanen da ke kamuwa da cutar korona da kuma mace-mace da ake ta yi wadanda suka wuce kima.

Ko da yake gwamnatin Kano ta ce ta dauki matakin ne domin bai wa mutane damar fita don sayen kayan abinci da na sauran bukatu, masana kiwon lafiya na ganin cewa sassauta dokar kullen ya yi wuri idan aka yi la'akari da ta'azzarar da cutar korona take yi a jihar.

Ya zuwa ranar 4 ga watan Mayu, Kano tana da jumullar mutum 342 da suka kamu da cutar korona, yayin da mutum takwas suka mutu, kuma ko mutum daya bai warke ba.
Hasalima ita ce ta biyu a duk fadin Najeriya cikin jihohin da suka fi fama da cutar.

Farfesa Usman Yusuf, tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta Najeriya kuma kwararren likita kan abin da ya shafi jini da bargon dan adam, ya shaida wa BBC cewa matakin sassauta dokar kullen ragon azanci ne musamman ganin yadda cutar korona take ci gaba da yaduwa.

"Ni a ganina ragon azanci ne bai wa mutane dama su fita ana tsaka da wannan annoba. Babu wata hujja a likitance da za ta sa gwamnatin Kano sassauta dokar hana fita a wannan lokacin. Misali, idan aka ce mutane su fita a wasu ranaku, za su samu damar haduwa da juna kuma tun da wannan kwayar cuta ba a daure take ba, za a kwaso ta sosai. Don haka wannan kuskure ne," a cewar Farfesa Yusuf.

Ya kara da cewa irin wannan sassauci ne ya haifar da mutuwar daruruwan miliyoyin mutane lokacin annobar Spanish flu da ta faru shekara fiye da dari da suka wuce.

"Abin da ya faru kenan lokacin Spanish flu. Da aka ce mutane su zauna a gida suka damu, sai gwamnati ta bar su su fito, inda suka yi ta kamuwa da cutar suna mutuwa. Hasalima, mutanen da suka mutu bayan an bar su sun fito sun fi mutuwar da aka samu a farkon cutar".

"Mu likitoci gaskiya kawai za mu fada babu ruwanmu da siyasa. Ya rage ruwan gwamnati ta bai wa mutane tallafin abinci ganin cewa kashi fiye 90 cikin dari na mutane ba su da abinci sai sun fito sun nemi abin da za su. Muhimmin abin yi shi ne a bar shiga cunkoso, kuma ba za a bar cunkoso ba sai gwamnati ta bai wa mutane abinci, a cewar tsohon shugaban hukumar inshorar lafiyar ta Najeriya.

A yi taka tsantsan

Shi ma Dr Abdulmumin Sa'ad, wani kwararren likita mai zaman kansa a kan cututtukan da ke yaduwa da ke da zama a Amurka, ya shaida wa BBC cewa sassautar dokar abu ne mai matukar wahala amma ya kamata a yi taka tsantsan wajen yin sausauci.

A cewarsa, "Idan za a sassauta dokar hana fita, ya kamata a yi la'akari da abubuwa da dama. Misali, ya dace a duba inda cutar take raguwa ta yadda idan aka bai wa mutane damar fita na wasu kwanaki, za su ci gaba da daukar matakan kare kansu daga kamuwa daga cutar".

"Ana yin kulle ne domin a hana cutar yaduwa sannan hukumomi su samu damar kintsa asibitoci da sauran wuraren killace mutane. Kuma ana sassauta dokar ne a hankali ta hanyar yin la'akari da wuraren da cutar ta fara raguwa," a cewar Dr Sa'ad.

Ya kara da cewa a yayin da aka sassauta dokar, za a ci gaba da gwaji sannan a dunga bibiyi wadanda suka yi mu'amala da masu dauke da cutar da kuma bayar da kariya ga ma'aikan lafiya da tabbatar da cewa kowanne dan kasa ya yi biyayya ga dokokin kare kai daga cutar.

A cewarsa akwai bukatar hukumomi su kara maida hankali wajen daukar matakan rage radadin kulle.


Dr Sa'ad ya kara da cewa idan ba a yi taka tsantsan ba to sassauta dokar ka iya janyo kara yaduwar korona a Kano.


 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Coronavirus: Mene ne illolin sassauta dokar kulle a Kano ?"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?