--
Sarautar Gargajiya: An nada sabon Shehun Bama, Alhaji Umar Ibn Kyari Al Amin El-Kanemi

Sarautar Gargajiya: An nada sabon Shehun Bama, Alhaji Umar Ibn Kyari Al Amin El-Kanemi

Rohoton: https://hausa.legit.ng

Alhaji Umar Ibn Kyari Al Amin El-Kanemi, babban dan marigayi Shehun Bama, Alhaji Kyari Ibn Umar Al Amin Ibn Ibrahim El Kanemi, ya zama sabon Shehun masarautar Bama.

Tawagar gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Jidda Shuwa, suka gabatar da wasikar ga sabon sarkin masarautar a ranar Litinin, 4 ga watan mayu, 2020.

Sauran mambobin tawagar sun hada da kwamishanan harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiya da Diraktan lamuran masarautu.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nada shi ne da sharadin cewa zai zauna a garin Bama ba ya rika mulkan al'ummarsa daga Maiduguri ba.

Sakataren gwamnatin jihar yace: "Mai girma (gwamna) ya umurceni da fada maka cewa ka zauna a Bama saboda ya nunawa jama'arka kana tare da su."

"Matsayinka na shugaba na da muhimmanci ga gudanar lamuran jama'a."

"Gwamnan jihar Borno ya nada ka ne saboda gaskiyarka da tarihin yiwa mutanen karamar hukumar Bama aiki."

"Ya kai mai martaba, wannan matsayi da gwamnan Borno ya nadaka, ana kyautata zaton za kayi adalci, daidaito da kyautatawa ga jama'an Bama."

Sakataren gwamnatin ya karkare da cewa an nada sabon Shehun ne bisa ga shawarar masu nada sarki na masarautar Bama. Gabanin nadasa, Shehu Umar, ya kasance dan kasuwa.

Yau ta cika mako daya da tsohon Shehun Baman ya rasu.

Ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiyan da yayi a asibitin koyarwan jamiar Maiduguri.


 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Sarautar Gargajiya: An nada sabon Shehun Bama, Alhaji Umar Ibn Kyari Al Amin El-Kanemi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?