LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Coronavirus: Kamfanonin da suka samu riba da asara lokacin cutarAnnobar cutar korona ta kawo durkushewar tattalin arziki amma dokokin kulle da suka taƙaita zirga-zirga sun taimaka wa wasu masana'antu wajen ci gaba.

Misali, mutane da yawa sun koma sayayya a shafukan intanet, kuma hakan ya kawo ci gaba sosai ga ɓangaren saye da sayarwa ta intanet.

Tabbas hakan ya taimaka wa wasu kamfanoni, amma alkaluman da ke fitowa daga babban kamfanin saye da sayarwa ta intanet na Amurka, Amazon, sun nuna cewa lamarin ba haka yake ba.

Karkashin jagorancin mutumin da ya fi kowa kudi a duniya, Jeff Bezos, Amazon ya yi suna a tsakiyar watan Afrilu a matsayin daya daga cikin wadanda suka amfana da annobar cutar korona, inda kwastomomi suka rika tururuwar shiga shafin suna kasha kusan dala 11,000 duk dakika daya.

Saboda haka, hannayen jarin kamfanin Amazon sun yi tashin da bas u taba yi ba.

Bayan mako biyu, zance ya sauya. An sanar da cewa kamfanin na iya yin asara a karon farko a shekaru biyar lokacin da za a sanar da cinikinsa na tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni.

Duk da kudin da ya samu tsakanin watan Janairu suwa Maris, Amazon na fuskantar bukatar kashe wasu kudi don tafi da harkokinsa saboda karuwar kwastomomi da ya samu inda har ya kara daukar ma'aikata 175,000.

Kamfanin y ace dole ya kashe dala biliyan 4 saboda cutar Covid-19 wajen samar da kayan kariya ga ma'aikatansa da yin feshin magungunan tsaftace muhalli a manyan wuraren ajiye kayayyakinsa.

Wannan kudi, ya yi dai-dai da ribar da kamfanin ya samu a watanni ukun farko na 2019 wato dala biliyan biyu da rabi.

Netflix ya jagoranci kallon fina-finai a intanet
vKamfanin samar da nisahdi ya samu ci gaba a lokacin wannan kulle, inda masu bibyarsa suka rika karuwa fiye da yadda suke a baya.

A shekarun da suka gabata, kallon fina-finai ta intanet ya shahara sosai.

Yayin da yawan mutanen da suka je silma kallon fina-finai ya karu da kasha 18 cikin 100 a shekaru biyu da suka gabata, masu kallon fina-finai a Netflix sun karu da kasha 47 cikin 100 a lokacin guda.

Bai zo da mamaki ba, da bangaren samar da nishadi ya samu ci gaba tunda mutane da yawa na kulle a gida.

"A Italiya da Sufaniya, misalim mutanen da suka fara amfani da Netflix a karon farko sun karu da kasha 57 cikin 100 da kasha 34 cikin 100 a lokacin kullen," in ji wani mai sharhi kan abubuwan da ke faruwa a intanet, Blake Morgan.

"Mutane na bukatar nishadi yanzu fiye da ko yaushe."

Ran 22 ga Afrilu, Netflix ya sanar da cewa ya samu sabbin kwastomomi miliyan 16 tsakanin watannin Janairu zuwa Maris.

Sai dai, wani hanzari ba gudu ba.

Yanayin kulle da aka shiga, ya dakatar da shirya sabbin fina-finai.

Haka kuma, darajar kudaden kasashe da dama ta ragu saboda annobar, hakan na nufin cewa sabbin masu bibiyar Netflix, ba wani kudi na a zo a gnai suke kawo wa kamfanin na kasar Amurka ba.

Wani babban kamfanin mai samar da fina-finan na Amurka, Disney, ya samu riba kuma ya yi asara a lokacin annobar.

Sai da ta kai kamfanin ya rufe wuraren shakatawarsa ruf, bayan da aka sa dokar kulle, kuma hakan ya jawo wa kamfanin asarar dala biliyan 1.4 a cewar shugabansa Bob Chapek.

Amma a halin da ake ciki, bukatar kallon fina-finai ta shafin Disney ya yi tashin gwauron zabi.

Duka-duka a watan Nuwamba aka kaddamar da shafin na Disney+ amma kawo yanzu yana da masu bibiya miliyan 55, yawan mutanen da aka kwashe shekaru bakwai kafin Netflix ya tara.

Matsalolin Zirga-Zirga
Kamar yadda za ku yi tunani, ciniki ta intanet na iya zama samun riba mai tsoka ka kamfanonin da ke kai sako har zuwa kofar gidan masu saye.

Amma lamarin ya fi karfin haka.

Kamfanonin kai sakonni na Amurka na Fedex da UPS, kamfanoni mafi girma a wannan bangare, sun nemi taimakon gwamnatin Amurka saboda matsalolin zirga-zirga dalilin kulle.

Ribar da kamfanin UPS ke samu ya ragu da kasha 26 cikin 100 a wannan shekara kawo yanzu.

Masu kai abinci gida
Haka ma bangaren isar da abinci gida, kullen ya zo masu a wani yanayi.

Gidajen cin abinci sun ci gaba da aiki a wasu kasashe a fadin duniya amma ba a zama a cikinsu a ci abincin.

Amma yayin da aka samu karuwar sayyayar kayan saw a da kayan masarufi a inatnet, sayen dafaffen abinci bai samu wannan nasarar ba.

Kamfanin dilllancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa kamfanonin isar da abinci a manyan kasuwannin Turai kamar Just Eat da Uber Eats sun fuskanci faduwa.

Mata masu zaman kansu, sun shiga mawuyacin hali

Daga Colombia zuwa Denmar, an samu karuwar masu sayen kayan da ake amfani da su wajen gamsar da kai lokacin saduwa a yayin kulle.

Babbar masana'anta ce mai girman kusan dalar Amurka biliyan 27 a shekarar 2019.

Amma barkewa cutar ta janyo wa mata masu zaman kansu asara sannan sun sake shiga hadarin kamuwa da cutar.

A kasashe da yawa, mata masu zaman kansu ba su da wasu hakkoki kuma gwamnati ba ta bas u agaji. Hakan na nufin talauci da ma rashin muhalli musamman a lokacin annobar.

Japan na daga cikin kasashen da suke bai wa mata masu zaman kansu agajin kudi lokacin annobar ta korona.

Motsa jiki yayin kulle
Takaita zirga-zirga da tafiye-tafiye na nufin mutane ba za su je wuraren motsa jiki ba, amma kuma, an samu karuwar mutane masu sayen kayan da ake mafani da su wajen motsa jiki a gida.

A Australiya, misali, an yi ta sayen kayan motsa jiki da yawa.

An kuma ga karuwa a bangaren na'urorin da ke taimakawa wajen motsa jiki.

Agogunan nan na Smartwatch sun samu riba da kasha 22 cikin 100 a farkon shekarar 2020 idan aka hada da farkon shekarar 2019, kamar yadda alkaluman kamfanin Strategy Analytics suka nuna.

"Mutane da yawa na amfani da smartwatch wajen sa ido kan lafiyarsu a lokacin wannan kullen,2 a cewar Steven Waltzer jami'I a kamfanin.

Amma kullen ya zo wa kwararru a bangaren motsa jiki da wahala. Shahararren kamfanin nan rukunin dakunan motsa a Indiya Cult fit ya sanar da cewa zai kori ma'aikata 800 kuma zai rufe wasu rassansa a fadin kasar, kuma za a rage wa sauran ma'aikatan da suka rage albashinsu da kasha 50 cikin 100.

Sadarwa ta Intanet
Yayin da miliyoyin mutane a fadin duniya ke aiki daga gida, shanyoyin sadarwa ta intanet sun kara shahara.

Cikin irin wadannan hanyoyin shi ne manhajar Zoom wadda ake iya shirya taro a kanta kuma har da hoton bidiyo.

A watan Afrilu, an sauke manhajar Zoom sau miliyan 131a cewar kamfanin bincike na Sensor Tower - kuma wannan na nufin yawan saukewar ya rubanya sau 60 idan aka hada da bara.

A cewar Sensor Tower, Indiya ce ke da kasha 18 cikin 100 na mutanen da suka sauke manhajar sai kuma Amurka da kasha 14 cikin 100.

Zoom ya zama hanyar da mafi yawan kamfanoni da masana'antu suka fi so su yi amfani da shi.

Yayin da mafi yawan mutane ke amfani da manhajar kyauta, Zoom na samun kudi daga masu amfani da shi da ke biya don samun wasu damarmaki, kuma kamfanin ya samu dala miliyan 122, ya rubanya abin da ya samu a daidai lokacin a bara.

Hannayen jarin Paypal
Daya daga cikin manyan kamfanonin biyan kudi na duniya, PayPal, ya yi matukar shiga mawuyacin hali dalilin Covid-19, inda gaba daya ribarsa a watanni ukun farko na 2020 ya ragu zuwa dala miliyan 84, wato asarar ta rubanya sau 8 idan aka hada da bara.

Amma kuma, darjar hannayen jarin PayPal ta yi karuwar da ba a taba gani ba ran 7 ga watan Mayu.

Ya masana kasuwanci ke kallon wannan?
Mutane da yawa na fuskantar matsin tattalin arziki kuma ba za su kasha kudi sosai ba a lokacin wannan kullen, amma kuma, yanayin na zaburar da su wajen komawa ga bangaren biyan kudi ta inatent.

PayPal ya samu sabbin masu rajista da shi miliyan 10 tsakanin watannin Janairu da maris kuma yawan kudin da ya yi aiki da su ya kai dala biliyan 199 - inda ya samu karuwar dala biliyan 161.5 a daidai wannan lokacin a shekarar 2019.

"Muna tunanin cewa mun kai wani mataki a fadin duniya inda mutane ke ganin cewa biyan kudi ta intanet na da matukar sauki," a cewar shugaban PayPal Dan Schulman.

"Wannan ba batun kulle ba ne. Akwai bincike daba-daban da ke nuna cewa a halin yanzu mutane sun fi son biyan kudi ta intanet maimakon sai sun je har shago," a cewarsa.KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments